Ƙalubalantar sakamakon wucin gadin zaɓen Gini | Labarai | DW | 03.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙalubalantar sakamakon wucin gadin zaɓen Gini

'Yan adawan ƙasar Gini suna zargin an tabka kura-kuari kuma an yi maguɗi a zaɓen majalisar dokokin da 'yan ƙasa suka daɗe suna hanƙoron ganin an gudanar.

A photograph made available 28 June 2010 shows a woman voting for presidential elections in Conakry, Guinea 27 June 2010. Around 4 million eligible voters went to the polls on 27 June in the small West African nation of Guinea to elect a new head of state. Twenty-four candidates are vying for votes in the first democratic election since independence from France in 1958. A run-off vote between the two most promising candidates is seen as likely. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++

Jamiyyun adawan ƙasar Gini sun ce ba za su amince da sakamakon wucin gadin da ake bayyanawa na zaɓen Majalisar dokokin da ƙasa ta daɗe tana begen ganin an gudanar ba, ta kuma sanar cewa za ta janye wakilanta daga cikin masu ƙidayar ƙuri'un da ake cikin yi yanzu.

Wannan sanarwa nata ya sanya ayar tambaya kan ko zaɓen wanda aka sa ran zai kasance mataki na ƙarshe na mayar da ƙasar bisa turbar demokraɗiyya, zai ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, har ma 'yan adawa su amince da sakamakon ƙarshe a matsayin halatacce.

kamfanin dillancin labaran Associated Press ya rawaito ɗaya daga cikin 'yan adawan, Sidya Toure, yana zargin cewa an sauya ƙuri'u, lokacin da ake kayan takardun zaɓen zuwa Conakry bayan da mahukunta suka sanar da sakamakon farko a yankunan Fria da Dubreka, wasu 'yan adawan ma sun ce an girka runfunan zaɓen boge guda 50 a cikin ƙasar, zargin da gwamnatin ta ƙaryata.

Rabon ƙasar Ginin da zaɓen majalisar dokoki dai tun shekara ta 2002, inda aka riƙa jinkirta zaɓen saboda yawan tarzoma da tashe-tashen hankula. Daga farko hukumar zaɓe ta ce za a sanar da sakamako bayan sao'i 72 yanzu an sake ɗage wannan wa'adin zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe