1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar yan jaridu ta ƙasa da ƙasa ta baiyana rahotonta na shekara

December 19, 2012

Shekara 2012 ta kasance ma fi muni ga yan jaridu na duniya inda aka kashe 88,kuma ƙasahen da lamarin ya fi ƙamari sune Siriya da Somaliya daMexiko da Pakistan

https://p.dw.com/p/175YP
Presseausweis © Alterfalter #25970264 -
Hoto: Fotolia

A rahotonta na shekara da ta baiyana ƙungiyar yan jaridu ta ƙasa da ƙasa Reporters sans frontières RSF,ta ce wanan shekara da ke shirin ƙarewa ta zama shekara mafi muni da aka samu kisa na yan jaridu wada ba a taɓa gann irinta ba tun a shekara ta 1995 .

Rahoton ya ce a wannan shekara an kashe kimanin yan' jaridu 88 a duniya abinda ya ƙaru da kashi 33 fiye da shekara da ta gabata.Yankunan da lamarin ya fi yin ƙamari sune na arewacin nahiyar Afirka inda aka kashe yan jaridu 26,sai yankin asiya na da 24 kana ƙasashe Afirka da ke a yankin kudu da hamada a can an kashe yan jaridu 15, sai Somaliya.Siriya a yankin gabas maso tsakiya ita ce ke kan gaba da yan jaridu 17, sai Pakistan da Mexiko da kuma Braziliya a sauran yankunan daban daban.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu