1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙungiyar yan adawa a ƙasar Ethiopia ta yi ƙorafin cewa akwai kura kurai a zaɓen yan' majalisun dokoki

May 23, 2010

Yan adawa sun zargi gwamnati a ƙasar Ethiopia da hana ma magoya bayansu saka ido a zaɓen yan' majalisun dokoki

https://p.dw.com/p/NVLA
Meles Zenawi shugaban gwamnatin ƙasar EthiopiaHoto: AP

 ƙungiyar yan adawa a ƙasar Ethiopia ta yi zargin cewa an hanawa magoya bayanta da ke saka ido a zaɓen yan majalisun dokoki da ke gudana a ƙasar a yau .Lura da yadda al amuran zaɓen ke wakana a yankin Oromiya inda nane cibiyar yan adawar.

Ɗan takara  jam'iyyar demokrate forum, Worku Feyirana ya bayyana cewa tsakanin ƙarfe shidda na safe zuwa ƙarfe tkwas da aka bude runfunan zaɓen ,sun yi la'akari da kura kurai da dama. .

Shima Ezachew Seferawe  ɗan takara haɗin gwiwa jamiyyun adawar a yanki Medrek ya yi korafi kamar cewa Ana yiwa yan takarasu barazana da ban tsoro.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita       :   Abdullahi tanko bala