1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙungiyar Eu da gudummowar soji a Afirka

Dugge, Marc / Rabat (HR) January 30, 2008

A ranar laraban nan ce ƙungiyar tarayyar Turai EU take fara wani gagarumin aikin soji mafi girma a cikin tarihinta

https://p.dw.com/p/CzCe
Wani sojin EUFOR na tarayyar TuraiHoto: AP

A gun wani taro da suka yi a birnin Brussels, ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar ta EU sun amince da tura sojoji kimanin dubu uku da 700 zuwa ƙasashen Chadi da Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, inda zasu gudanar aikin wanzar da zaman lafiya.


Daga cikin shugabanni da fitattu a duniya da suka ziyarci sansanonin ´yan gudun hijira dake gabacin ƙasar Chadi akwai Angelique Kidjo shahararriyar mawaƙiyar nan ´yar ƙasar Benin. Angelique Kidjo ita ce wakiliyar Asusun Taimakon Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNICEF a takaice, ta yi bayanin irin abubuwan da ta ganewa idon ta a sansanin ´yan gudun hijira.


Angelique Kidjo ta ce "Abin da na ganin musamman ya tabbatar da abubuwan da na ji kafin in kai wannan ziyara. Ana ci-gaba da aikata laifuka daban-daban ciki har da yiwa mata fyade, harbe mazansu da ´ya´yansu har lahira sai kuma jariri ɗan kwanki 40 da haihuwa wanda aka yi masa yankan rago. Ban san tsawon lokacin da zan ɗauka kafin in manta da wannan ta´asa ba."


Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ke kula da sansanonin ´yan gudun hijirar a ƙasar Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Dubun dubatan ´yan ƙasar Sudan da wasu ´yan Afirka Ta Tsakiya da kuma wasu ´yan gudun hijira daga Chadi suke kwarara zuwa sansanonin da samun mafaka, abinci da kariya daga ta´asar ƙungiyoyin ´yan banga masu ɗaukar makami waɗanda har yanzu suke zama barazana ga ´yan gudun hijirar. Suna kuma yiwa ƙungiyoyin agaji sace-sace. To yanzu dai ana sa rai nan ba da jimawa ba dakarun rundunar EUFOR na ƙungiyar tarayyar Turai EU zasu taimaka a kawo ƙarshen wannan aika-aika sannan a wani dogon lokaci zasu taimakawa ´yan gudun hijira komawa gidajensu. Jan Peter Stellema na ƙungiyar likitoci masu ba da agaji a gabacin Chadi ya yi nuni da cewa.


Stellema ya ce "Idan da sukuni ´yan gudun hijirar sun fi son su koma gida inda zasu ci-gaba da aikinsu kamar noma da kiwo da renon ´ya´yansu. Suna son su koma ga tafiyar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a da cikin sauki ba tare da wata tsangwama ba.To sai dai hakan ba zai yiwu ba sai an samu cikakken tsaro."


Sojoji dubu uku da 700 na rundunar EUFOR zasu gudanar da aikin samar da zaman lafiya da tsaro. Fiye da rabinsu sojojin Faransa ne. Ita kuwa Jamus ba zata ba da gudunmawar soja ba to sai dai gwamnati a Berlin zata taimaka da kuɗin tafiyar da wannan aiki. Faransan ce kuma ta cike giɓin da aka samu na wasu ƙasashe inda ta ba da ƙarin sojoji da motoci da jiragen sama da alikoptoci. Idan ba haka ba kuwa da wannan aikin wanda aka shirya farawa a cikin watan Nuwamban bara ba zai yiwu ba. Ganin cewa sojojin Faransa sun fi yawa to haka ka iya zama wata matsala, domin ɗaukacin ´yan ƙasar Chadi suna sukar lamirin tsohuwar uwargijiyar ta su musamman a dangane da goyon bayan da gwamnati a Paris take bawa shugaba Idris Deby, wanda ba ya da farin jini a Chadi. Abin kunyar nan da ya shafi ƙungiyar agaji ta Faransa wato Arche de Zoe ya ƙarawa Faransa baƙin jini. Annete Rehrl ta hukumar ´yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Chadi ta yi nuni da cewa.


Rehrle ta ce "Idan ana son wannan rundunar ta samu nasarar tafiyar da aikinta na ba da kariyar ga fararen hula da sauran ´yan agaji, to dole a ɗaga murya a faɗa musu cewa ka da su zo kasar nan da nufin kare shugaban kasa. Ka da su tsoma bakinsu a harkokin cikin gida na Chadi."


To sai dai lokacin da ya rage don yin irin wannan kira kaɗan ne. Domin tun daga yau sojojin ƙasar Austriya za su fara zuwa yankin.