1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin Obasanjo a rikicin Cote d'Ivoire

January 10, 2011

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kyautata fatan samun mafita daga rikicin siyasar Cote d'Ivoire.

https://p.dw.com/p/zvwJ
Olusegun Obsanjo mai shiga tsakani a Cote d'IvoireHoto: AP

Tuni dai tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bar ƙasar Cote d'Ivoire bayan da ya yi ƙoƙarin shawo kan Shugaba Laurent Gabagbo da ya yi ƙememe ya ƙi sauka daga karagar mulki, da ya sauka a cikin limana. A yayin ganawar da ya yi da ɓangarorin biyu Obasanjo ya nuna buƙatar daukar matakan da suka dace domin warware rikicin siyasar da ya kunno kai bayan zaƙen shugaban ƙasar inda yake cewa:

"A duk sanda matsala ta taso ana buƙatar ɗaukar matakai daban daban ne domin warware ta tare da zaɓar matakin gaskiya mai inganci. Ya zuwa yanzu dai ina kyauata fatan samun mafita daga wannan rikici a cikin ruwan sanyi."

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi