Zuma ya ce ba ya tsoron shiga gidan kaso | Labarai | DW | 05.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuma ya ce ba ya tsoron shiga gidan kaso

Yayin da jama'a a ciki da wajen Jam'iyyar ANC mai mulki ke kara matsin lamba ga Jacob Zuma ya sauka daga karagar mulki kan zargin cin hanci, shugaban yace ba ya tsoron shiga gidan kaso

Shugaban Afirka ta Kudu jacob Zuma da ke fama da dambarwar siyasa ya shaidawa wani taron magoya bayan Jam'iyyarsa ta ANC a garin Dumbe a mahaifarsa dake Kwazulu-Natal cewa ba ya tsoron zuwa gidan yari dangane da zargin cin hancin da ake masa

"Ya ce ko da za'a kama ni a yau, na saba da shiga gidan kaso, an daure ni a kurkuku tsawon shekaru goma tare da Nelson Mandela saboda haka ba za'a bani tsoro da gidan yari ba."

A ranar Larabar da ta gabata ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Afirka ta kudu ta yi kira ga masu gabatar da kara su binciki zargin almundahana, a yayin da ta wallafa rahotonta kan Zuma wanda ya kara rura wutar kiraye-kiraye a ciki da wajen jam'iyyar ANC ga shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa.

Hukumar binciken dai ta maida hankalinta ne a kan zargin Zuma ya bada dama ga iyalan Gupta, hamshakan attajirai 'yan kasar India wajen yin tasiri a cikin gwamnati ciki har da ba su damar zabar wadanda za'a nada a mukaman Ministoci.