Zuma: Majalisa na kada kuri′ar tsige shi | Labarai | DW | 10.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuma: Majalisa na kada kuri'ar tsige shi

Jam'iyyar adawa ta Demokratic Alliance ce ta gabatar da bukatar 'yan majalisar Afrika ta Kudu kada kuri'ar yiwuwar tsige shugaba Zuma

A wannan Alhamis din ce 'yan majalisar wakilan Afrika ta Kudu ke kada kuri'ar yiwuwar tsige shugaba Jacob Zuma. To sai dai bisa dukkan alamu shugaban zai tsira, duk da irin matsinn lamba da bacin rai da jam'iyyarsa ta ANC ke fuskanta.

Tsawon lokacin da yake kan karagar mulki dai, Zuma ya cimma tsallake rigingimu masu dabaibayi, kuma a makon da ya gabata ya fuskanci karin matsin lamba dangane sabbin zargi na cin hanci.

Mai shekaru 74, wanda ya karbi mulki tun a shekara ta 2009, na samun tagomashi tsakanin 'yan jam'iyyarsa ta ANC da 'yan majalisa da masu fafutukar kare siyasa musamman mazauna karkara.

Jam'iyyar adawa ta Demokratic Alliance ce ta gabatar da bukatar kada kuri'ar tsige Jacob Zuma, kan abunda ta kira " cin zarafin jaririyar demokradiyyar kasar ta Afirka ta Kudu".