Zuba jari a sashen wutar lantarkin Nijeriya | Labarai | DW | 26.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuba jari a sashen wutar lantarkin Nijeriya

Jonathan ya ce baiwa 'yan kasuwa damar zuba jari a sha'anin wutar lantarki ne zai warware ƙarancin wutar a ƙasar

default

Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana sabuwar manufar da gwamnatin sa za ta aiwatar ga sashen wutar lantarkin ƙasar, wanda ya tanadi baiwa 'yan kasuwa - masu zaman kansu damar sanya hannun jarin su a ɓangaren, wanda cin hanci da rashawa ya yiwa katutu, kana matsalar ta janyo yawan ɗauke wutar lantarkin a cikin ƙasar.

Shugaba Jonathan wanda ya bayyana sabon shirin a birnin Lagos cibiyar kasuwancin Nijeriya ya ce sassan samar da wutar da kuma rarraba ta ne hukumomin za su cefanar ga 'yan kasuwa a hannu guda, a yayin da a ɗaya hannun kuma gwamnatin za ta bunƙasa yin amfani da iskar gas wajen tafiyar da wasu sabbin cibiyoyin samar da wutar.

Shugaban ya ƙaddamar da sabon shirin ne a lokacin da babban bankin ƙasar ya bayar da kuɗi Naira miliyan dubu 300 domin tallafawa batun zuba - jari a sashen wutar lantarkin da kuma na sufurin jiragen sama.

Hakanan matakin ya zo ne jim kaɗan bayan mummunan ta'asirin da yajin aikin ma'aikatan hukumar kula da harkokin wutar lantarkin ya yiwa tattalin arziƙin ƙasar dama na jamhuriyyar Nijar, wadda ke samun wani kaso na wutar daga Nijeriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammed