1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zuba Jari a Afurka

Kamfanonin jamus sun fara sha'awar zuba jari a Afurka

default

Shugaban Senegal Abdoulaye Wade.

A baya-baya nan dai kamfanonin Jamus ke bayyana sha’awarsu na zuba jari a kasashen Afurka. Dangane da haka aka gudanar da wani taro a birnin Frankfurt karkashin taken: Ranar zuba jari a Afurka. Wani da ake kira Hanson Sindowe daga kasar Zambiya, a yanzu haka ‘yan kasuwa na haba-haba da shi domin kulla huldar cinikayya da kamfaninsa na wutar lantarki. Daga baya-bayan nan kungiyar taimakon raya kasa ta Jamus ta gabatarwa da kamfanin nasa na Copperbelt Energy Corporation taimakon tsabar kudi euro miliyan takwas, wadanda zai yi amfani da su wajen sabunta ayyukan kamfanin. Amma fa duk da haka Hanson Sindowe, bar dadara ba yana famar neman karin ‘yan kasuwa na ketare da zasu zuba jari a kamfaninsa ta yadda zai samu kafar ba da wutar lantarki ga sassa daban-daban na kasar Zambiya. Hanson Sindowe ya ce:

“Akwai kafa iri daban-daban a kasar Zambiya. Duk wani kamfanin da zai zuba jari a harkar samar da wutar lantarki zai iya sayar da wutar ga kasashe makobta, saboda kamfanoni da yawa dake aiki a wadannan kasashe suna fama da karancin wutar lantarki.”

A wasu ‘yan tsirarun shekaru da suka wuce ‘yan kasuwa sun sha yi wa Hanson Sindowe ba’a, lokacin da kamfaninsa ke dab da fuskantar fatara saboda bijirewar da ‘yan kasuwa na ketare suka yi masa. Daidai da Hanson Sindowe shi ma Jürgen Thumann, shugaban kungiyar masana’antun Jamus, a halin yanzu haka ya dokata da ire-iren damar dake akwai a Afurka wajen zuba jari. Thumann yayi bayani yana mai cewar:

“Al’amuran tattalin arziki da siyasa na tafiya salin-alin, kuma ana dada samun kyawawan kafofi na zuba jari a Afurka. Da yawa daga cikin kasashen nahiyar na samun bunkasar da ta zarce ta kashi 6% ga tattalin arzikinsu, suna masu kawo canje-canje da samar da kyakyawan yanayin zuba jari.”

Wani babban misali a game da wannan ci gaba shi ne kasar Ghana, wadda take bakin kokarinta wajen ganin ta kayyade yawan matalauta ‘yan rabbana ka wadata mu a kasar da misalin kashi 50% na da shekara ta 2015. An saurara daga ministan kudi na kasar Kwado Baah-Wiredu cewar zuba jarin kamfanonin ketare kawai ba shi ne zai taimaka a cimma wannan manufa ba. Ministan ya kara da cewar:

“Ala-kulli halin dai kasashe zasu ci gaba da dangantakar ciniki tsakaninsu, amma abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da adalci a wannan hulda. Idan muka dauka misali a shekaru 50 da suka wuce buhun koko daya zai iya saya maka motar marsandi biyu, amma a yau ko rabin motar ma ba zai iya saya maka ba, zamu gane cewar lamarin da walakin, babu adalci a cikinsa kuma wajibi ne a yi gyara.