Ziyarar Westerwelle a Turkiyya | Labarai | DW | 28.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Westerwelle a Turkiyya

Yau ministan harkokin wajen Jamus ke kai ziyara a Turkiyya

default

Guido Westerwelle, ministan harkokin wajen Jamus.

A yau ne ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle zai kai ziyara a ƙasar Turkiyya inda zai tattauna tare da takwaransa na wannan ƙasa, Ahmet Davu-toglu. Ana sa rai minstocin biyu za su tattauna tayin da Iran ta yi a baya-bayan nan, game da tattaunawar da ake akan shirinta na nukiliya. Za su kuma yi magana game da burin Turkiyya na zama mamba ta Ƙungiyar Tarayyar Turai. A jiya Talata, Westerwelle ya faɗa wa jaridar Bild ta Jamus cewa Turkiyya ba ta yi tanadin haɗewa da Ƙungiya Tarayyar Turai ba. Amma kuma ya nanata cewa bai kamata ba, ƙasashen ƙungiyar su yi watsi da ita. Fraministan Birtaniya, David Cameron ya ci alwashin ba da goyon bayansa ga Turkiyya a ƙoƙarinta na zama mamba ta Ƙungiyar Tarayyar Turai. A yayin ziyarar tasa Westerwelle zai kuma gana da Firaminista Recep Tayyip Erdogan.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu