Ziyarar Westerwelle a China | Siyasa | DW | 15.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Westerwelle a China

A yau Juma´a ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yana birnin Beijing a ziyararsa ta farko ƙasar China.

default

Guido Westerwelle da Yang Jiechi

Daga cikin batutuwan da yake mayar da hankali kansu a tattaunawarsa da hukumomin ƙasar har da batun ingantan kare haƙƙin ɗan Adam da ´yancin faɗin albarkacin baki. A tattaunawar da ya yi da takwaransa na China Yang Jiechi, Westerwelle ya ce sassan biyu sun bayyana ra´ayoyinsu dangane da batun yankin Tibet.

Ko da yake a ganawarsa da takwaransa na China Yang Jiechi, ministan harkokin wajen na Jamus Guido Westerwelle ya goyi bayan faɗaɗa harkokin cinikaiya tsakanin ƙasashen biyu, amma kuma bai ƙi taɓo batun kare haƙin ɗan Adam ba yana mai cewa duk da saɓanin ra´ayin tsakanin Jamus da China akan wannan batu amma bai kamata a yi shiru ba.

"Takwaran aiki na ya san cewa kare haƙin ɗan Adam da kariya ga tsirar da ´yancin ´yan jarida da faɗan albarkacin baki da kuma ´yancin addini, muhimman batutuwa ne a manufofinmu da ƙetare. A tsanake na taɓo waɗannan batutuwan a tattaunawar da muka yi."

Westerwelle ya ƙara da cewa sun taɓo batun yankin Tibet da na shugaban addinin yankin wato Dalai Lama a tattaunawar su, inda suka bayana ra´ayinsu ko da yake sun saɓawa juna. Ministan harkokin wajen China Yang Jiechi ya nunar a fili cewa ga China Dalai Lama wani shugaba ne na siyasa wanda ƙasar ta Sin ba za ta amince da ƙoƙarinsa na nemawa yankin Tibet ´yanci ba. A nasa ɓangaren Westerwelle ya jaddada manufar Jamus kan China inda ya mika goron gayyata ga takwaran na sa na zuwa taro kan al´amuran tsaro da zai gudana birnin Munich a cikin watan Fabrairu. Yang ya karɓi wannan goron gayyatar da hannu bi-biyu.

Duk da kyakkyawan yanayi da aka gani a wannan ziyara, amma tun ba yau hulɗar dangantaka tsakanin Jamus da China ba ta tafiya salim-alim kamar yadda take a da.

Tun a shekarar 1972 ƙasashen biyu suka ƙullar hulɗar diplomasia tsakaninsu, kuma an sha faɗi tashi. A halin da ake ciki China ce babbar abokiyar hulɗar cinikaiya da Jamus a jerin ƙasashen nahiyar Asiya. Baya ga hulɗar ciniki ƙasashen biyu na musayar ra´ayoyi na siyasa. Liu Liqun na fannin harsunan ƙetare a jami´ar birnin Beijing masani ne kan harkokin Jamus, ya yi maraba da wannan ziyara da Westerwelle ke kaiwa China.

"Kasancewa a cikin watanni uku bayan samun muƙamin ministan harkokin waje Westerwelle ya kawowa China ziyara. Hakan na nuna cewa sabuwar gwamnatin Jamus da ministan harkokin wajenta na ɗaukar China da muhimmanci. Duk da cewa a Jamus ana rubuta bayanan ɓatanci akan sa, amma mu a China muna girmama shi."

Ana sa rai ministan harkokin wajen na Jamus ɗan jam´iyar FDP zai kuma taɓo batun gidauniyar Friedrich Naumann wadda a shekarar 1996 hukumomin China suka rufe ofisoshinta dake Beijing saboda tana marawa Dalai Lama baya. Har yanzu kuwa hukumomin China na zargin gidauniyar da goyawa ´yan awaren yankin Tibet baya.

Mawallafa: Petra Aldenrath/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal