1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Steinmeier ga China

Kasar China ce zangon karshe ga ziyarar yini biyar da ministan harkokin wajen Jamus ke yi a Asiya

Steinmeier da Li Zhaoxiang

Steinmeier da Li Zhaoxiang

A lokacin taron manema labarai da ya biyo bayan ganawar da yayi tare da P/M Wen Jiabao da ministan harkokin waje Li Zhaoxiang, Frank-Walter Steinmeier ya fito fili ya bayyana matsalolin dake akwai ba tare da wata rufa-rufa ba. Daya daga cikin batutuwan da aka mayar da hankali kansu kuwa shi ne matsayin gwamnatin China dangane da maganar kare hakkin mawallafa ko na kirkire-kirkire. Steinmeier ya kara da cewar:

Dangantakar tattalin arziki na tafiya salin-alin tsakanin kasashen biyu, kamar yadda aka ji daga bakin takwarana. Amma dukkanmu mun hakikance cewar dangantakar tattalin arzikin na bukatar wata kyakkyawar madogara domin samun ci gaba. A sabili da haka dukkan kasashen biyu ke bukatar ganin an cimma daidaituwa domin shawo kan sabanin da ake fama da shi akan kare hakkin mawallafa.

Wannan maganar ka iya zama wata sabuwar manufa ta tuntubar juna tsakanin China da Jamus. Dukkan kasashen biyu dai na da shirin tuntubar juna akai-akai tsakanin gaggan jami’an siyasarsu domin tattauna wasu muhimman batutuwa kamar dai kare hakkin jama’a a kasar China, lamarin da aka tabo a lokacin ganawar tsakanin Steinmeier da jami’an siyasar Chinar. A nata bangaren kasar ta China ta bayyana sha’awar sanin matsayin da ake dangane da takunkumin haramta sayar mata da makamai da KTT ta kakaba mata. A zamanin baya dai tsofon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder yayi alkawarin sa baki domin ganin a soke wannan takunkumi. Steinmeier dai ya fito fili ya bayyana wa shuagabannin Chinar cewar Jamus ba zata sayarwa da kasar makamai ba saboda dokar cinikin makamai ta kasar ba ta amince da haka ba. A baya ga wadannan batutuwa jami’an siyasar sun mayar da hankalinsu ga matsaloli na kasa da kasa kamar dai famar kai ruwa ranar da ake yi dangane da shirin nukiliyar kasar Iran. To sai dai kuma ko da yake Steinmeier bai fida kaunar kakaba wa Iran takunkumi in har zarafi ya kama ba, takwaransa Li Zhaoxiang ya ki ya bayyana ko ita ma China a nata bangaren a shirye take ta goyi bayan irin wannan mataki na takunkumi. Li ya ce a halin da ake ciki yanzun wannan magana ba ta taso ba tilas ne a dakaci rahoton da hukumar makamashi ta kasa da kasa zata bayar a cikin watan maris mai zuwa. Duk da sabanin ra’ayin dake akwai tsakanin China da Jamus akan wasu batutuwan, amma dangantakarsu na tafiya salin-alin ba tare da wata tangarda ba, in ji Steinmeier, wanda ya kara da cewar:

Ta la’akari da kakkarfar huldar dake tsakaninmu ba ma shayin tattauna dukkan abubuwan da ka hana ruwa gudu kuma zamu ci gaba akan hakan har kwanan gobe.