Ziyarar Steinmeier a yankin gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 15.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Steinmeier a yankin gabas ta tsakiya

Ministan harkokin wajen Jamus da takwaransa na Jordan,a Amman.

Ministan harkokin wajen Jamus da takwaransa na Jordan,a Amman.

Sarki Abdallah na kasar Jordan yayi kira ga kasashen turai dasu taimaka wajen sake ginin kasar Lebanon,tare da kare sake barkewan wani rikici a yankin baki daya.

Sarki Abdallah na biyu,wanda yayi wannan rokon a tattaunawarsa da ministan harkokin waje na Jamus Frank-Walter Steinmeier dake rangadin aiki a yankin na gabas ta tsakiya,yace Berlin da sauran fadojin gwamnatin kasashen turai nada da muhimmiyar rawa da zasu taka wajen sake ginin Lebanon ,tare da tallafawa alummar kasar da taimakon da suke bukata a halin yanzu.

Kazalika yakumayi kira ga alummomin kasashen duniya dasu dauki matakai na kare barkewan kowane irin rikici a yankin gabas ta tsakiya,tare da jaddada cewa tushen zaman lafiya a yankin dai ya dogara ne da samarwa palasdinawa yancin cin gashin kansu.

Basaraken yace halin da yankin ya tsinci kanshi ciki ,na bayyana bukatar tallafin kasashen duniya na kare shi daga fadawa cikin wani wadi na tsaka mai wuya makamancin wannan.Sarki Abdallah yace samarwa alummar Palasdinawa yantacciyar yancin kai,shine abu mafi muhimmanci wajen gano bakin zaren warware rigingimu dake dabaibaye yankin baki daya.

A jawabinsa tunda farko ministan harkokin wajen na Jamus steinmeier,ya bayyanawa sarki Abdallah na biyu,irin kokarin da kungiyar gamayyar kasashen turai tayi na cimma tsagaita wuta tsakanin Izraela da yan Hizbollah na Lebanon,bayan fafatawa na wata guda.

Babban jakadan na Jamus wanda ya isa birnin Amman tun jiya da maraice,ya soke ziyarar dayake shirin kaiwa kasar syria da yammacin yau ,bayan kammala rangadinsa a Jordan dake makwabtaka.

Soke ziyarar ta sa kuwa nada nasaba ne da kalaman shugaba Bashar al-Assad na Syrian,inda ya bayyana izraela da kasancewa makiya,a jawabin da yayi yau da rana.

Steinmeier yace kalaman na Assad nada illoli sosai a kokarin da ake na samarda zaman lafiya a yankin.

A jawabin nasa dai shugaba Assad,yace samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya zai zame abu mawuyaci,kuma Amurkace zaa zarga kann hakan.

Shugaban Syrian mai shekaru 40 da haihuwa,ya fadawa taron manema labaru a birnin Damascus cewa ,dole Izraela ta mikawa larabawa filayensu data mamaye tun daga shekarata 1967,ko kuma ta cigaba da fuskantar kyama.

Rangadin na Steinmeier ,wanda ke zama na uku cikin tsukin wata guda a yankin,nada nufin neman hadin kann kasashen yankin wajen samarda dorarriyar zaman lafiya a kasar Lebanon.

Sakamakon soke ziyarar tasa zuwa Syria,anasaran ministan harkokin wajen na Jamusa zai wuce kasar Saudi Arabia yau.

 • Kwanan wata 15.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyj
 • Kwanan wata 15.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyj