1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Steinmeier a Washington

Ziyarar ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier a Washington ita ce ta farko da wani ministan harkokin wajen wata ƙasar Turai ga Amirka bayan sauyin gwamnati a fadar White House

default

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier

A lokacin ziyarar, Steinmeier zai gana da takwarar aikinsa ta Amirka Hillary Clinton. Bisa ga dukkan alamu Frank-Walter Steinmeier yana alla-alla ya san sabbin manufofin Amirka game da ƙasashen ƙetare. Duk da cewa a ranar Asabar mai zuwa sabon mataimakin shugaban Amirka Joe Biden zai yi jawabi kan wannan batu a zaman babban taron duniya kan harkokin tsaro a birnin Munich na nan Jamus, amma mista Steinmeier ya fara wannan gajeriyar ziyara ga sabuwar takwarar aikinsa ta Amirka Hillary Clinton bisa dalilin cewa sabuwar ajandar ƙasa da ƙasa na buƙatar ɗaukar matakan gaggawa na bai ɗaya tsakanin Amirka da Turai.

Ministocin biyu za su tattauna akan jerin batutuwa kama daga batun sauyin yanayi, makamashi, halin da ake ciki a Iraqi, matsalolin tattalin arzikin duniya har izuwa ga batun taron ƙolin ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da za a yi a cikin watan Afrilu mai zuwa. Majiyoyin tawagar ministan harkokin wajen sun ce Steinmeier zai kuma nemi Clinton da ta ƙoƙarta wajen rage tsamin dangantaka tsakanin Amirka da Rasha. A game da batun kwance ɗamarar yaƙi kuwa Steinmeier cewa yayi.

Ya ce: "Batutuwa kamar wannan abu ne da ba za mu nuna gajiyawa ba don tattaunawa da sabuwar gwamnatin Amirka. Haka ya kasance a farkon ziyarar Obama zuwa Berlin, da kuma hirar ta wayar tarho da na yi da sabuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka."

Steinmeier na mai ra´ayin cewa ana nuna son kai a rahotannin da ake bugawa a Jamus game da Obama.

Ya ce: "A nan ina kira ga masu mayar da hankali kaɗai ga rahotannin dake cewa Obama zai tura ƙarin sojoji Afghanistan, da su bari mu dubi abin da idanun basira. Kamata yayi sun san cewa an shiga sabon babi na kyautatuwar hulɗa tsakanin Jamus da Amira saɓani yadda ake gani a fili."

Wannan ziyara ta Steinmeier zuwa Washington na matsayin cike wani buri a harkokin siyasar cikin gida, domin a bayyane yake irin ƙoƙarin da Steinmeier ke yi na kusantar sabuwar gwamnatin Amirka, musamman ta hanyar aikewa da buɗaɗɗiyar wasiƙa shugaba Barack Obama da tayin da Jamus ta yi na karɓar firsinoni daga sansanin Guantanamo. Steinmeier dai na gina wata gada ce ga Washington yayin da shugabar gwamnati Angele Merkel ta ke ɗariɗari da ɗaukar irin wannan mataki. Ko da yake ba a shirya wata ganawa tsakanin Steinmeier da Obama ba, amma ko shakka babu duk wani kacibis da za su yi da sabon shugaban na Amirka zai ɗaga darajar ɗan takarar na neman shugabancin gwamnatin Jamus ƙarƙashin inuwar jam´iyar SPD.

Sauti da bidiyo akan labarin