1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Steinmeier a Ghana

ƙasashen Jamus da Ghana sun jaddada cewa tura sojin haɗaka na Afrika da Majalisar ɗinkin duniya domin aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur shi kaɗai ba zai warware rikicin yankin da yaƙi ci yaƙi cinyewa ba. Ministan harkokin wajen Jamus Farank Walter Steinmeier wanda ya kai rangadi zuwa ƙasar Ghana, bayan ganawa da takwaran aikin sa na ƙasar Gahanan Akwasi Osei Adjei sun baiyana fatan taron da zai gudana a ƙasar Tanzania a tsakanin yan tawayen Dafur da manzon musamman na Majalisar ɗinkin duniya zai share fagen kawo ƙarshen rikicin baki ɗaya. Ministocin biyu na harkokin waje suka ce matakan soji ba zasu kasance masalaha ga yanayin tsaro a Dafur ba. Suka ce muhimmin abin da ya kamata shine tattaunawa da dukkan ɓangarorin domin warware taƙaddar cikin ruwan sanyi. Ministan harkokin wajen na Jamus Frank Walter Steinmeier na cigaba da ziyarar aiki ne a Ghana a zango na biyu na rangadin ƙasashen nahiyar Afrika da yake yi. Tun da farko Steinmeier ya gana da shugaban Nigeria Umaru Musa Yar Aduá a birnin tarayya Abuja inda ya yabawa ƙoƙarin Nigeriar na sasanta rigingimu a tsakanin yankunan Afrika.