Ziyarar Singh a Nigeria | Labarai | DW | 15.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Singh a Nigeria

Nigeria da India zasu rattaba hannu akan yarjejeniyar tsaro da wasu muhimman yarjejeniyoyi guda auku ,dazai inganta dangantakara bangarorin biyu,ayayin rangadin aikin permier Manmohan Singh.Kasashen biyu dai sun cimma mincewa kafa ofisocin hulda na ketare,ayayinda nan da watanni shida masu gabatowa kasashen biyu zasau kammala yarjejeniyar inganta tare da samardsa da kariya na harkokin kasuwanci,way an kasuwan su.Premiern Indian ya bayyana cewa yana fatan ganin ingantuwan dangantakar kasuwanci da Nigeria,wadda ke kasancewa uwa mabada mama a Afrika,wadda kuma take da albarkatun man Petur.Mai Shekaru 75 da haihuwa,Manmohan Singh na muradin ganin cewa albarktun kasa da Afrika kedasu ,sun taimawa tattalin arzikin India dake cigaba da bunkasa.Nigeria dai na mai zama babbar Aminiyar kasuwancin India a nahiyar Afrika.A yan watanni da suka gabata nedai India da Singh suka samu izinin hakar rijiyoyin mai a tarayyar ta nigeria,wanda kuma ya dada inganta huldodin kasuwancinsu.