Ziyarar Shuganba Hu a Afrika | Siyasa | DW | 30.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Shuganba Hu a Afrika

Ayau ne shugaban kasar Sin yake fara rangadin aiki a nahiyar Afrika

Shugab Hu Jin tao na kasar Sin

Shugab Hu Jin tao na kasar Sin

A yau ne shugaban kasar Sin Hu Jintao ya fara rangadin aikin kwanaki 12,dazai kashi kasashe 8 na nahiyar Afrika,inda batutuwan kisan kiyashi da mai da bunkasan harkokin kasuwanci zasu mamaye rangadin nasa.

Ziyarar ta shuga Hu wanda ke kasancewar na ukun irinsa a nahiyar Afrika da hawansa karagar mulki a shekarata 2003,wanda kuma ke bangaren kokarin kasar ta Sin na inganta dangantakar siyasa da tattali da kasashen wannan nahiya.

Da take jaddada manufofinta wa Afrika Sin a jiya litinin ta bayyana cewa zata yafewa wasu kasashen Afrika kimanin 33 basussuka datake binsu ,a bangaren alkawarin makuddan kudade da tace zata kashe akan wannan nahiya domin farfasdo da ita daga kangin da take ciki.

Wannan sabuwar danganta da kasar ta Sin ta kulla da Afrika dai ya samu suka daga kasashen yammaci na turai,musamman bisa ganibn yadda kasar ke cigaba dayin tasiri cikin harkokin kasuwannancin wadannan kasashe.

Ayayinda yan kasuwan turai din keyiwa kamfanonin Sin kallon masu samun kwangila na cin moriyar akbarkatun da Allah ya huwacewa nahiyar Afrika,kungiyoyin kare hakkin jamaa da wasdu gwamnatoci na zargin Sin din da hada kai da gwamnatocin da ake zargi da take hakkin bil adama.

Sai dai kawo yanzu kasar Sin din bata nemi gafara adangane da dangantarta na harkokin soji da sdiyasa da tattalin arziki da gwamnatocin nahiyar ta Afrika ba,duk da kasashen da turan sukayi Allah wadansu kamar Sudan da Zimbabwe.

Akan wannan kallon da kasashen turan kewa Sin ne shugaban kasar Botswana Festus Mogae yace,Sin tana daidaita kanta da Afrika,ba kamar sauran kasasshen turai dake musu kallon waddanda ke baya har yanzu ba,kuma akan hakan ne yake maraba da sinawan a kullum......

A yau din dai ministan tsaro na Sin ta bakin kakakin maaikatar harkokin wajen kasar Jiang Yu ya kare kasarsa dacewa cikin adalci da gaskiya suke tafiyar da wannan dangantaka tasu ,kuma bashi da nufin lahani wa kasashe matalasuta da suke hulda dasu.

Mr Jiang yace duzkkan makamai da kasar Sin take saidawa Afrika ,yana bisa kaidojin kasa da kasa.

Shima premiern kasar Habasha Meles Zenawi cewa yayi ,kasar ta Sin tana da dama a halin yanzu na taimakawa kasashen Afrika wajen farfado da tattalin arfzikinsu,kuma tuni a yanzu haka aka fara ganin tasirin hakan.

Shugaba Hu Jintao dai zai fara yada zango ne a kasar kameru,kana duk da korafin kasashen turai a ranar jumaa zai isa kasar Sudan,a matsayin kasata uku a wannan rangadin aiki nasa da zata kaishi ga Zambia da Namibia da Afrika ta kudu da Mozambique da kuma tsibirin Seychelles.

Makasudun wannan ziyarar shugaban na Sin dai shine cigaba da inganta dangantakar farfado da tattalin arziki.

 • Kwanan wata 30.01.2007
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwT
 • Kwanan wata 30.01.2007
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwT