1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugabar Liberia zuwa Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeNovember 29, 2005

A yau zababbiyar shugabar Liberia take fara ziyarar kawance zuwa wasu kasashen yankin Afrika ta yamma

https://p.dw.com/p/Bu3q
Ellen Johnson Sirleaf
Ellen Johnson SirleafHoto: AP

Wannan itace ziyararta ta farko tun lokacin da aka zabi Ellen johnson mace ta farko shugabar kasa a nahiyar Afrika.

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ya tarbe tare da wasu manyan jamiansa a filin jirgin saman birnin Abidjan.Wannan ziyara a cewar mai magana da yawun Johnson, an shirya tana ne da nufin karfafa dangantakar Liberia da makwabtanta.

Ana sa ran shugabar ta Liberia zata wuce zuwa kasashen Nigeria Saliyo da Guinea.

A makon da ya gabata ne aka tabbatar samun nasarar Ellen Johnson a zabe na farko tun bayan yakin basasan kasar,wadda abokin adawarta dan wasan kwallon kafa, George weah yake ikrarin an tafka magudi a cikinsa,duk da cewa masu sa ido a zaben na kasa da kasa sunce zaben ya gudana cikin yanci da adalci.

Kasashen Liberia da Ivory coast dai suna farfadowa daga yake yaken basasa wadanda suka hada da yara kanana dauke da makamai suna shiga kungiyoyin tawaye daban dabam tsakanin kasashen biyu.

Sabuwar shugabar kasar ta Liberia tace zasu duba batutuwa da zasu sake karfafa tsaro da kwanciyar hankalin kasashen biyu.

Tun da farko jamaa da dama sun dauki kasar Liberia a matsayin kasa mafi rikici a yankin afrika ta yamma musamman ma karkashin shugabancin tsohon madugun yan tawaye Charles Taylor wanda ake zargi da haddasa fitunu a yankin, wanda yanzu haka yanzu haka yake zaman gudun hijira a Nigeria.

Kotun dake da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a Saliyo tana zargin Taylor da aikata laifukan yaki haka zalika kasar Guinea ta zarge shi da hannu cikin yunkurin kashe shugabanta.

A yanzu haka kungiyoyin kare hakkin bil dama sun baiyana cewa ana daukar sabbin mayaka yan Liberia domi suyi fada a kasar Ivory Coast.

Shugaba Ellen itace shugaba ta farko a Liberia da zata taba ziyartar kasashen Guinea Saliyo da Ivory Coast,tun karshen yakin basasar kasar.

Yayainda kasar Liberia take kokarin tsamo kanta daga yakin basasa na shekaru 14,shirin zaman lafiya na Ivory Coast ya sami cikas musamman game da cece kuce da akeyi kan shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na baya bayan nan.

Tun farko ya kamata waadin Gbagbo ya kare a ranar 30 ga watan oktoba,amma kudirin Majalisar ya amince masa karin tsawon shekara guda bisa karagar mulki,inda zai shirya sabon zabe a kasar da ta rarrabe tsakanin yan tawaye dake arewacin kasar da gwamnati dake kudu kana da dakarun wanzar da zaman lafiya dake tsakiyarta.

A halin yanzu dai a watan janairu na shekara mai zuwa idan Allah ya kai mu zaa rantsar da sabuwar shugabar ta Liberia.