Ziyarar shugabar Jamus a Indiya | Labarai | DW | 31.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugabar Jamus a Indiya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shiga kwana na biyu na ziyarata a kasar Indiya inda a yau ta gana da wasu yan wasa da kuma kwararru na kasar ,nan gaba a yau zata wuce babban birnin kasuwanci na kasar Mumbai.A ranar talata Merkel tace kasashen Jamus da Indiya sun shirya ribanya harkokin kasuwanci tsakaninsu da kusan euro biliyan 20 a kowace shekara,har zuwa shekaru 5.Shugabar ta Jamsu tana magana ne ga manema labarai a birnin New Delhi bayan ganawarta da firaministan Indiya Manmohan Singh.Tace wasu bangarori kuma da zaa inganta dangantaka kansu sun hada da kimiya da magance dumamar yanayi.Firaminista Singh ya baiyana wannan shiri a matsayin wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Jamus da Indiya.Sun dai sanya hannu kann yarjeniyoyi 7 na karafafa dangantaka tsakani.Wannan dai shine karo na farko da shugabar gwamnatin Jamus ta kai ziyara kasar India.