1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR SHUGABAN TARAYYAR JAMUS JOHANNES RAU A NAHIYAR AFIRKA

YAHAYA AHMEDMarch 15, 2004

Tun ran 16 zuwa ran 24 ga wannan watan ne shugaban kasar Jamus Johannes Rau zai kai ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka. Zai fara ya da zango ne a Najeriya, inda zai ziyarrci biranen Abuja da Kano. Daga nan ne kuma zai ziyarci kasar Tanzaniya.

https://p.dw.com/p/BvlI
Shugaban Kasar Jamus, Johannes Rau
Shugaban Kasar Jamus, Johannes RauHoto: AP

Game da ziyarar da zai kai a Afirka, shugaban kasar Tarayyar Jamus, Johannes Rau ya bayyana cewa:-

"Na yi imanin cewa, wannan ziyarar tana da muhimmanci kwarai, musamman ma ga Jamus. A halin yanzu dai duniya ta zamo kamar wani kauye. Shi ya sa mu Jamusawa ma, wajibi ne gare mu mu bayyana ra’ayinmu a wannaN kauyen. Mai yiwuwa ya zamo abin fa’ida ga wasu. Sabili da haka ne nake wannan tafiyar, duk da sanin cewa, ina begen fara hutu na, bayan na sauka daga mukamin da nake rike da shi a halin yanzu."

Wannan ziyarar a nahiyar Afirka dai, ita ce ziyarar aiki ta karshe da shugaba Johannes Rau zai kai a mukaminsa na shugaban kasa, kafin barin mukamin a karshen wa’adin aikinsa a cikin watan Mayu. Kasashen da zai ziyyarcin kuwa su ne Najeriya, da Tanzaniya. Zai kuma ya da zango a kasar Jibuti, a kan hanyarsa zuwa gida. Kasashen da shugaban zai kai wa ziyara dai suna da muhimmanci kwarai ga huldodin da Jamus ke da su a nahiyar ta Afirka. Kamar yadda Stefan Mair na gidauniyar kimiyya da siyasa da ke birnin Berlin ya bayyanar:-

"Bayan Afirka Ta Kudu, Najeriya ce muhimmiyar abokiyar huldar Jamus a nahiyar, musamman ma dai a harkokin man fetur."

Johannes Rau zai yi kwana biyu ne a Najeriya. A ranar farko zai kasance ne a Abuja. Sa’annan kashe gari kuma, zai ziyarci birnin Kano, daya daga cikin biranen kasar da ke da yawan musulmi. Wasu alkaluma dai na nuna cewa akwai a kalla musulmi miliyan 50 zuwa 60 a Najeriya. Wannan adadin kuwa ya fi na ko wace kasa a nahiyar ta Afirka.

Yunkuirn da Najeriya ke yi a halin yanzu, na ganin an samad da zaman lafiya a yankin Afirka Ta Yamma, ya sami amincewar Jamus kwarai da gaske. Stefan Mair ya bayyana cewa, matakan da shugaba Obasanjo ke dauka game da wannan batun na samun cikakken goyon bayan Jamus. Ya kara da cewa:-

"Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirkka kalilan da suka mai da hankali kan wannan batun na samad da zaman lafiya a nahiyar. Tana kuma taka muhimmiyar rawar gani, kamar dai yadda misalan Laberiya da kuma Saliyo ke nunawa."

Daga Najeriyan dai, shugaban zai ci gaba da ziyararsa ne zuwa kasar Tanzaniya. Ita dai wannan kasar tana da arzikin namun daji da kuma wuraren yawon shakatawa masu ban sha’awa, kamarsu gandun namun dajin nan na Serengeti da kuma tsaunin nan na Kilimanjaro, mafi tsayi a nahiyar. Game da huldar da ke tsakanin Tanzaniyan da Jamus kuwa, Mair ya bayyana cewa:-

"Tanzania dai ita ce kasar da Jamus ta fi bai wa muhimmanci a huskar ba da taimakon raya kasashe a nahiyar ta Afirka. Tun dai fiye da shekaru 30 ko 40 kke nan da Jamus ke da kyakyawar ma’ammala da kasar ta Tanzaniya."

Kasar ta Tanzainya dai tana daya daga cikin kasashe matalauta na nahiyar Afirkan. Amma duuk da haka tana taka muhimmiyar rawar gani a yankin gabashin Afirka.

Shugaba Rau zai yi kwana hudu ne a kasar, inda zai yi shawarwari da shugaba Banjamin Mkapa, sa’annan kuma ya gana da shugaban kotun kasa da kasa da ke shari’ar `yan kisan kiyashin Ruwanda. Zai kuma ziyarci gandun namun dajin kasar, don ya gano wa idanunsa irin albarkatun halittar da Tanzaniyan ke da su.