ZIYARAR SHUGABAN TARAYYAR JAMUS, HORST KÖHLER, A KASAR SALIYO. | Siyasa | DW | 08.12.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR SHUGABAN TARAYYAR JAMUS, HORST KÖHLER, A KASAR SALIYO.

A ziyarar da yake kai wa kasar Saliyo, shugaban tarayyar Jamus ya halarci shagulgula daban-daban a birnin Freetown. Ya kuma yi wa taron majalisar dokokin kasar jawabi, inda ya nanata shirin Jamus na bai wa wannan kasa taimako.

Shugaban tarayyar Jamus, Horst Köhler

Shugaban tarayyar Jamus, Horst Köhler

Saliyo dai ba wata kasa ce a nahiyar Afirka, wadda za a nuna ta don yin kwaikwayo da irin rawar da ta taka ba. Amma a bangare daya kuma, kasar ta yi iyakacin kokarinta, wajen farfado da kafofin siyasa da kuma kwance wa mayakan kungiyoyi daban-daban damara, bayan yakin basasan da kasar ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da shi.

A ziyarar da shugaban tarayyar Jamus, Horst Köhler, ya kai a wannan kasar dai, ya tuntubi nuna wa al’umman Saliyo din zumunci da kuma karfafa musu gwiwa a yunkurin da suke yi na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga duk jama’ar kasar. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin Freetown, shugaba Köhler, ya bayyana cewa, kowa dai ya iso kasar, zai ga alamun famar da take yi na shawo kan matsalolin da yakin basasan ya haifar mata. Ya kara da cewa:-

"A nawa kiyasin dai, an sami ci gaba a kasar bayan wannan mummunan yakin. Amma duk da haka, da akwai ayyuka da yawa a gaba, da ya kamata a ci karfinsu. Mun san dai alhaki ya rataya a wuyar gwamnatin kasar, da ta tabbatar da ganin cewa, an nuna wa wadanda aka ci zarafinsu adalci. Kazalika kuma, kamata ya yi Gamayyar Kasa da Kasa ta tallafa mata da kudade don farfado da tattalin arzikinta. Idan na koma Berlin zan ba da bayanin abin da na gano wa idanuna, musamman ma dai na cewar kasar ta Saliyo tana bukatar taimako cikin gaggawa, don shawo kan matsalolin da suka kunno kai bayan yakin basasan."

Ban da dai taimako daga ketare, ba za aiya aiwatad da shirye-shiryen samad da zaman lafiya a kasar ba. A cikin shekara mai zuwa ne dai, wa’adin sojojin kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar zai cika. Bisa dukkan alamu dai, ba za a tsawaita wannan wa’adin ya kunshi yawan dakaru kamar na yanzu ba. Su dai shugabannin kasar ta Saliyo, sun kyautata zaton cewa, wannan ziyarar da shugaba Köhler ya kawo musu, zai share fagen janyo hankullan masu zuba jari a kasar, don farfado da tattalin arzikinta.

A halin yanzu dai, Saliyon ta tsunduma cikin matsaloli da yawa. Mafi yawan al’umman kasar, suna rayuwa ne da kasa da dolar Amirka daya a ko wace rana. Kasar kuma, ita ce ta karshe a jerin kasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta lassafta, masu fama da matsaloli iri-iri, wadanda kuma ,in ba da taimakon ketare ba, ba za ta iya fitowa daga kangin wahalhalun da suka rataya a wuyarta ba. Kusan kashi 70 zuwa 80 cikin dari na la’umman kasar ne ba su da aikin yi. Wannan hali na talauci da al’umman kasar suka sami kansu a ciki kuwa, zai iya zamowa wani tushe na barkewar tashe-tashen hankulla a kasar.

A ganawar da shugaba Köhler ya yi da alkalan kotun Majalisar Dinkin Duniya a birnin Freetown dai, an bayyana masa cewa, a halin yanzu ana shari’a ne kan kararraki guda 9.

Ana kuma dai kokarin kwance wa mayakan kungiyoyin da suka yi yakin basasan kasar damara, karkashin wani shirin da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar. Kusan mayaka dubu 70 ne wannan shirin ya shafa. Amma kawo yanzu kadan daga cikinsu ne suka sami aikin yi don iya ciyad da iyalansu.

A cikin jawabin da shugaba Köhler ya yi wa Majalisar dokokin kasar dai, ya karfafa cewa, Jamus za ta ci gaba da tallafa wa Saliyon, iya gwargwado. A cewarsa dai, babu wani bangaren duniya na farko, ko na biyu, ko na uku. Dukkanmu a kan doron kasa daya muke.

 • Kwanan wata 08.12.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveH
 • Kwanan wata 08.12.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveH