ZIYARAR SHUGABAN KASAR MALI A NAN JAMUS. | Siyasa | DW | 16.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR SHUGABAN KASAR MALI A NAN JAMUS.

A cikin wannan makonn ne shhugaban kasar Mali, Amadou Toumani Touré, ya kawo ziyara a nan Jamus. Duk da yanayin sanyi da aka shiga ciki, har da dusar kankarar da ta rufe titunan birnin Berlin, yayin da ya sauko, shugaban na Mali ya bayyana farin cikinsa da irin karbar bakwancin da gwamnatin Jamus ta yi masa:

"Ina matukar farin ciki da gayyatar da aka yi mini na zo nan. Ina kuma farin ciki da kyakyawar dangantakar da ke tsakaninmu da Jamus. Na dai gamsu kwarai da irin kyakyawan marhaban da aka yi mini.

A cikin wasu `yan makwannin da suka wuce ne, ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer ya kai wata ziyara a kasar ta Mali. Yayin wannan ziyarar ne kuma, ya gayyaci shugaban kasar Malin zuwa nan Jamus. Bayan zagayawar da aka yi da shi a cikin birnin Berlin dai, shugaba Toumani Touré ya bayyana cewa:

"Ai abin kayataswa ne kwarai, yawon da muka yi cikin hadaddiyar Berlin, ba tare da ganin wata katanga kuma da ta raba birnin a sassa biyu ba. Wannan dai na tabbatad da cewa, an kammala hidimomin hadewar Jamus a zahiri. Na gamsu kwarai da kyau da tsarin birnin Berlin." Jamus dai, ita ce farkon kasar da ta amince da Malin a nan nahiyar Turai, bayan samun `yancinta. Shugaba Touré ya bayyana cewa, tun wannan lokacinn ne kuma, aka fara huldodin dangantaka tsakanin kasashen biyu. Abin da kuma sai kara ingantuwa yake yi. Mali dai ta nuna wa Jamus yadda take daukar wannan dangantakar da muhimmanci, yayin da a cikin watan Agustan da ya gabata, ta yi duk iyakacin kokarinta wajen ganin cewa, an cim ma sako `yan garkuwa 14 nan na kasashen Yamma, wadanda akka yi wa lakabin `yan garkuwan Sahara. Game da kokarin da Mali ta yi a kan wannan batun dai, shugaba Touré ya bayyana cewa.

"Ba mu yi wata-wata ba, wajen tsai da shawarar mai da martani ga duk alherin da Jamus ta yi mana. Yayin da aka bukaci taimakonmu wajen warware matsalar `yan garkuwar, mun amsa wannan kiran ne da hannu biyu-biyu. Saboda mun san cewa, duk da kasancewar yunkurin wani babban kalubale garemu, za mu iya kuma ta hakan karfafa yarda da ke tsakanin kasashenmu."

Jamus dai ta nuna matukar farin cikinta ga irin rawar da Malin ta taka wajen cim ma sako `yan garkuwar. Sabili da hakan ne kuwa, gwamnatin tarayya ta kara yawan taimakon da za ta bai wa kasar ta yammacin Afirka da kashi 25 cikin dari. A halin yanzu dai taimakon da Jamus ke bai wa Malin ya kai kimanin Euro miliyan 71 da digo 5.

Da yake jawabi a wata liyafar ban girma da aka shirya wa shugaba Touré, a fadar Bellevue da ke birnin Berlin, shugaban tarayyar Jamus, Johannes Rau, ya ce kasar Mali, ta yi nisa wajen bin tafarkin dimukradiyya a nahiyar Afirka. A nasa ganin ma, za ta iya zamowa misali ga sauran kasashen nahiyar.

A nasa bangaren, shugaba Toumani Touré ya tabbatar wa Jamus da sauran kasashen Yamma cewa, a shirye kasarsa take ta ba da tata gudummuwa wajen samad da zaman lafiya a duniya baki daya.kasar Mali dai ta taka muhimmiyar rawar gani a yunkurin da ake yi na samad da zaman lafiya a kasar Saliyo. Ta kuma ba da gudummuwar soji ga rundunar kare zaman lafiya a kasar laberiya, inji shugaban. A karshe dai, shugaban ya kyautata zaton cewa, nan gaba, kasarsa da Jamus za su karfafa wa juna gwiwa, wajen yakan ta'addanci.
 • Kwanan wata 16.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvn3
 • Kwanan wata 16.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvn3