Ziyarar shugaban kasar Jamus a nahiyar Afrika | Labarai | DW | 03.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaban kasar Jamus a nahiyar Afrika

Shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya fara ziyarar rangadi ta kwanaki goma a kasashen kudancin Afrika. Horst Köhler ya fara yada zango yau a kasar Mozambique inda ya gana da shugaban kasar Armando Guebuza. Horst Köhler wanda ke tare da rakiyar yan kasuwar kasar Jamus ya jinjinawa tafarkin dimokradiya a kasar Mozambique bisa aiwatar da tsari na jamíyu da dama. Ziyarar shugaban kasar ta Jamus na daga cikin yunkurin karfafa dangantaka tsakanin Nahiyar turai da kasashen Afrika. Daga Mozambique Horst Köhler zai wuce zuwa kasashen Madagascar da kuma Botswana. Köhler wanda tsohon shugaban Asusun bada lamuni ne na duniya IMF ya ziyarci nahiyar Afrika a shekara ta 2004. A kuma shekarar da ta gabata, ya gudanar da taro a nan Jamus tare da shugabannin kasashen Afrika a karkashin shirin kyautata alaka da zumunta da kasashen Afrika