Ziyarar shugaban kasar Jamus a Ghana | Labarai | DW | 12.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaban kasar Jamus a Ghana

Shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler yayi kira ga kasashen Afirka da su yi aiki tare da takwarorinsu na Turai don matsa kaimi a kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a Somalia da sauran yankunan da ake fama da rikici a nahiyar Afirka. Köhler ya yi wannan kira ne yayin wani taro da shugaban Ghana John Kufour a birnin Accra. Yanzu haka dai shugaban na Jamus yana wata ziyarar aiki ta yini hudu a Ghana. A na sa bangaren shugaba Kufour ya yaba da taimakon raya kasa da Jamus ke baiwa kasar Ghana, wanda a bara ya haura Euro miliyan dubu daya.