1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban kasar Jamus a DW

December 9, 2006

A ziyarar da ya kawo ga DW shugaban kasar Jamus yayi kira da a kara mayar da hankali ga nahiyar Afurka a cikin hira da Miodrag Soric yayi da shi

https://p.dw.com/p/Btx9
Köhler a DW
Köhler a DWHoto: B. Frommann

To Miodrag Soric ya fara ne da tambayar shugaban kasar ta Jamus Horst Köhler a game da ko shin mene ne ra’ayinsa a game da alhakin da ya rataya a wuyan Deutsche Welle a halin yanzu haka? Shi kuma sai ya kada baki ya ce:

Köhler:

“A dai halin da ake ciki yanzu babban alhakin dake kan tashar ta Deutsche Welle shi ne wayar da kan mutane a sassa daban-daban na duniya a game da manufofin Jamus da matsayinta a siyasa da tattalin arzikin duniya da kuma irin kyakkyawan zama na cude-ni-in-cude-ka dake akwai tsakanin jinsunan mutane masu banbance-banbancen al’adu a kasar. Wato dai ba da cikakken bayani a game da yadda kasar take ba ragi ba kari. Jamus dai tayi suna matuka ainun a matsayin kasa mai kakkarfan matsayin tattalin arziki kuma Deutsche Welle zata iya taka muhimmiyar rawa wajen kara daga martabar kasar a idanun duniya.”

Horst Köhler dai shi ne wani shugaban Jamus na farko da mayar da nahiyar Afurka ta zama ginshikin manufofinsa na ketare, inda ya kirkiro wata gidauniyar tallafa wa Afurka. To ko mene ne dalilin da ya sanya shugaban kasar na Jamus yake ba wa nahiyar Afurka irin wannan muhimmanci?

Köhler:

“Na nakalci matsalolin Afurka kai tsaye, kama daga matsalar yunwa zuwa ga bala’i daga Indallahi da rikice-rikice na cikin gida. A huldodina na yau da kullum a fannoni na siyasa da zamantakewa akan yawaita tabo maganar Afurka, inda wasu ke tunanin cewar tuni aka bar wannan nahiya a baya. Amma wannan tunanin in har ya tabbata a zukatan jama’a zai zama mummunar illa ga makomar nahiyar ta Afurka saboda mutane zasu ci gaba da watsi da irin ci gaban da kasashen nahiyar ke samu. Sako-sako da matsalolin Afurka zai iya haifar da mummunan radadi ga nahiyar Turai mai makobtaka da ita. A ganina nahiyar Turai na da wani alhaki na tarihi da ya rataya a wuyanta a game da makomar Afurka kuma wajibi ne ta cika wannan alhaki domin ta haka ne kawai ita ma a nata bangaren zata samu karbuwa.”

Deutsche Welle na taka muhimmiyar rawa a kokarin kyautata dangantaka da fahimtar juna tare da kasashen musulmi, inda a baya ga shirye-shirye na rediyo tashar take kuma gabatar da shirye-shirye na telebijin da yanar gizo domin wadannan kasashe. Shin a ganinka hakan ya dace?

Köhler:

“Kwarai da gaske. Domin kuwa a wannan bangaren muna fama da matsaloli, musamman a kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya. Amma na yi imanin cewar akwai yiwuwar samun zaman lafiya. Muhimmin sharadin cimma hakan kuwa shi ne fahimtar juna. Wani abin da zai taimaka game da haka shi ne, misali, kyautata zama na cude-ni-in-cude-ka da kuma dangantakar al’adu tare da abokan tarayyar mu musulmi dake nan kasar. Hakan na iya zama ginshikin manufofi na ketare da zai kai ga cimma biyan bukata, kuma a wannan bangaren Deutsche Welle na taka muhimmiyar rawa domin cike gibin dake akwai da dangantaka da kasashen Larabawa.”