1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban kasar Jamus a Afurka

March 29, 2006

A karo na biyu Horst Köhler zai kai ziyara Afurka tun daga 2 zuwa 12 ga watan afrilu

https://p.dw.com/p/Bu0x
Horst Köhler a Benin
Horst Köhler a BeninHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Kasashe uku da shugaban kasar Jamus Horst ya zaba domin kai musu ziyara a nahiyar Afurka, wadanda kamar yadda aka ji bayani tun farko suka hada da Muzambik da Madagaskar da Botswana sun taka muhimmiyar rawa a ‚yan tsirarun shekarun da suka wuce wajen tsame kansu daga matsaloli na talauci da cututtuka da karancin ilmin da kasashe da dama na nahiyar ke fama da su yanzu haka. Shugaban kasar na Jamus ya sikankance cewar akwai abubuwa da dama da kasashen Turai zasu iya koya daga nahiyar Afurka. A matsayinsa na shugaban asusun bayar da lamuni na IMF Horst Köhler ya ziyarci Afurka har sau shida yana mai bin diddigin ci gaban da nahiyar ke samu a fannoni na siyasa da tattalin arziki. A wannan karon ma, daidai da ziyarar da ya kai ga kasashen Saliyo da Benin da kuma Habasha a shekara ta 2004, shugaban kasar na Jamus ba ya da niyyar gabatarwa da kasashen da zai ziyarta wata takamaimiyar shawara a game da alkiblar da ya kamata su fuskanta. Domin kuwa bisa ga ra’ayinsa kamar yadda ya fada akan hanyarsa ta dawowa gida daga waccan ziyarar da ya kai, hakan ba abu ne da ya dace ba. Köhler ya kara da cewar:

„Wani abin da ko kadan bai kamata mu rika yi ba shi ne, mu rika yi wa kasashen Afurka shisshigi domin tilasta musu bin manufofi ko ra’ayoyinmu sakamakon taimakon kudi da muke bayarwa. Nahiyar Afurka tana da nata al’adun da mummunan tarihinta na bakin ciki, wanda ya hada da cinikin bayi da mulkin mallaka da radadin cacar baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin Turai. A saboda haka ya zama wajibi a saurara mata a kuma kyale ta domin ta samu kafar fuskantar alkiblar da ta dace da makomarta. Ala-ayyi-halin dai wajibi ne mu dakatar da kokarinmu na neman cusa wa al’umar Afurka ra’ayoyinmu game da rayuwa.“

Dukkan kasashen da Köhler zai kai wa ziyara kuwa sun fuskanci alkiblar da ta dace da su ne domin magance matsalolinsu na talauci da siyasa da tattalin arziki. Kyakkyawan misali a nan kuwa shi ne irin ci gaban da kasar Botswana ta samu bisa manufa. Kasar, wacce aka kwatanta ta tamkar kasar Switzerland a tsakanin kasashen Afurka ba ta dogara akan taimakon raya kasa daga ketare ba. Kasar na samun kyakkyawan ci gaba a matakanta na garambawul, lamarin da ba shakka shugaban kasar Jamus Horst Köhler, zai yaba mata a game da shi a ziyarar tasa. Botswana dai tafi kowace kasa ta nahiyar Afurka yawan kudaden shiga idan an kwatanta da jumullar abin da take samarwa a shekara, inda a shekarar da ta gabata ta samu bunkasar kashi biyar cikin dari ga tattalin arzikinta.

Dangane da ragowar kasashe biyun da Köhler zai yada zango a cikinsu kuwa, wadanda suka hada da Muzambik da Madagaskar, suma suna samun kyakkyawan ci gaba akan hanyarsu ta canjin manufofi ko da yake bas u da gwaggwaban tattalin arziki kamar Botswana kuma suna samun akasarin taimakonsu ne daga Jamus. Amma gaba daya dukkan kasashen guda uku sun cancanci da a kwatanta su a matsayin kasashe masu bin sahihin tsarin demokradiya da kuma kwanciyar hankali, kuma bisa ra’ayin Köhler kasashe ne da suka zama abin koyi, wadanda ke ba da kwarin guiwa a game da makomar nahiyar Afurka. Domin kuwa canje-canjen demokradiyya daga tushensa shi ne sharadin samun ci gaba a nahiyar Afurka.