1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban kasar a China

September 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuAs

Shugaban ƙasar Chadi Idriss Deby Itno ya fara ziyarar rangadi ta kwanaki huɗu a ƙasar China inda ake sa ran zai sanya hannu a kan yarjejeniyar cinikayya ta mai da iskar gas ya kuma tattauna da shugaban ƙasar Sin Hu Jin Tao a game da rikicin Dafur. Ƙungiyoyi masu fafutukar kare haƙƙin bil Adama sun zargi China da cewa ta ƙi matasawa gwamnatin Sudan ta datakar tarzomar dake faruwa a dafur don kawai tana kwaɗayin kare muradun ta na mai a Sudan din. Idriss Deby zai kuma sanya wata yarjejeniyar a Beijin da kamfanonin ƙasar Sin a fannin haƙar mai dana makamashi da kuma Siminti. Chadi muhimmiyar ƙasa ce dake da albarkatun mai yayin da a waje guda kuma China ke ƙoƙarin ƙara yin angizon ta a nahiyar Afrika. Ƙasashen biyu sun maida hulɗar jakadanci a tsakanin su ne a shekarar 2006, bayan tsawon shekaru tara suna zaman doya da manja.