1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban Faransa Sarkozy a China

November 25, 2007
https://p.dw.com/p/CSwr
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya fara wata ziyarar aiki a ƙasar China. Yanzu haka dai ya isa a birnin Xian mai daɗaɗɗen tarihi kafin ya ƙarasa zuwa Beijing inda zai tattauna da shugaban China Hu Jintao. A lokacin wannan ziyara ta kwanaki uku Sarkozy zai shaida bukukuwan sanya hannu kan yarjeniyoyi cinikaiya ciki har da ta shirin sayar da ƙarafen nukiliya na Faransa don samar da wutar lantarki da kuma ta sayen jiragen sama. Jaridar ƙasar Faransa La Tribune ta ce kamfanonin jiragen sama na China ka iya yin odar jiragen sama guda 150 samfurin Airbus da ake kerawa a Turai. Mai bawa Sarkozy shawara ya ce shugaban zai yi kokarin shiga tsakanin don maido da kyawawan dangantaku da suka yi rauni tsakanin China da wasu kasashen yamma. A cikin watan satumba China ta fusata dangane da ganawar da aka yi tsakanin Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da jagoran Tibet Dalai Lama, wanda China ke ɗaukarsa a matsayin ɗan aware.