Ziyarar shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a Aljeriya | Labarai | DW | 04.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a Aljeriya

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya yi suka da kakkausar harshen da mulkin mallakar da ƙasarsa ta yiwa Aljeriya da cewa rashin adalci ne. Kalaman na mista Sarkozy na matsayin wani mataki na sasantawa tsakanin Faransa da Aljeriya. Yayin da yake magana a gaban manyan manyan ´yan kasuwa na Faransa da Aljeriya a birnin Aljiyas Sarkozy ya ba da sanarwar cewa za a sanya hannu kan kwangilolin gina hanyoyin sadarwa da tashoshin samar da makamashi da kuɗin su ya kai euro miliyan dubu 5. Shugaban na Faransa dai yana wata ziyarar aiki ta kwanaki uku ne a Aljeriya.