Ziyarar Shugaban ƙasar Jamus a Turkiyya | Labarai | DW | 22.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Shugaban ƙasar Jamus a Turkiyya

Yau shugaban ƙasar Jamus, Christian Wulff ke kammala ziyarar mako gida da ya kai Turkiyya.

default

Christian Wulff, ta hagu, da Abdullah Gul, da matansu.

 Yau shugaban ƙasar Jamus, Christian Wulff ke kawo ƙarshen ziyarar  da ya kai  Turkkiya, wadda ya ce ta yi armashi. Wulff ya ce ya gano irin yarda da Turkiya ta yi da Jamus a tsawon ziyarar tasa ta mako guda. Ya ƙara da cewa an cimma yarjeniyoyi game da wasu lamura da suka danganci siyasa.  Da safiyar yau, sai da Wullf ya gana da shugaban cocin gargajiya ta ƙasar Turkiya, Batholomew na Farko a birnin Istanbul . Yayin wannan ziyara, Wullf ya yi kira da a ƙara tabbatar da walwala da 'yancin addini ga Kristocin ƙasar ta Turkiyya .Yayin wata liyafa da takwaransa Abdullah Gül ya shirya domin nuna girmamawa gareshi, Wulff ya nuna goyon bayansa ga Turkiya a ƙoƙarinta  na zama mamba ta Ƙungiyar Tarayar Turai. Yau ne yake  kammala wannan ziyara tasa wadda ita ce irinta ta farko da wani shugaban ƙasar Jamus ya kai Turkiya cikin sama da shekaru goma da suka gabata. Kafin ya dawo gida Jamus  ana sa rai cewa Wulff zai sa tubalen gina jami'ar haɗin-gwiwa tsakanin  Jamus da Turkiyya tare da takwaransa Abdullah Gül.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Zainab Mohammed Abubakar