Ziyarar shugaban ƙasar Jamus a Paraguay | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaban ƙasar Jamus a Paraguay

Shugaban ƙasar Jamus Horst Köhler na cigaba da ziyara a ƙasar Paraguay inda ya fara yada zango a rangadin kwanaki goma sha biyu da zai yi a yankin kudancin Amurka. Da yake jawabi bayan ganawa da shugaban kasar ta Paraguay Nicanor Duarte frutos, Köhler ya baiyana buƙatar dake akwai ga dukkan alúmomi su ci moriyar shirin cigaban tattalin arziki na duniya. Yana mai cewa talauci shi ne babban abin da ke haddasa munanan laifuka da kuma ayyukan tarzoma. A saboda haka ya yi kira ga shugabanin siyasa dana tattalin arziki su himmatu wajen kyautata walwala da daidaito a tsakanin alúma.