1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugaban Ƙasar Sin a Afrika

Zainab MohammedFebruary 10, 2009

Hu Jintao zai ziyarci wasu ƙasashen Afrika huɗu

https://p.dw.com/p/Gr4c
Sarki Abdallah da Hu JintaoHoto: AP

Ƙokarin da ƙasar Sin keyi na tabbatar da matsayinta na jagora a lokacin da duniya ke cikin hali mawuyaci na tattali, ya juya akala zuwa nahiyar Afrika, inda a wannan makon ne shugaba Hu Jintao zai ziyarci wasu kasashen nahiyar.

Bayan kammala ziyararsa ta kwanaki uku a ƙasar Saudi Arabiya mai albarkatun man petur, shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin zai shige zuwa Mali da senegal da Tanzania sa'annan ya karasa rangadin nasa da Mauritius.

Dukkannin ƙasashen dai na bada damar bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin ne, duk dacewar ba sa cikin ƙasashen Afrika masu karfin tattalin arziki.

Chinesischer Präsident Hu Jintao in Afrika
Hu Jintao da Paul BiyaHoto: picture-alliance/ dpa

Harkokin kasuwanci tsakanin Ƙasashen Nahiyar Afrika da Sin dai ya haɓaka zuwa kimanin dala billiyan 107 a shekarar data gabata, kuma wannan ziyara ta Shugaba Hu na nuni dacewar manufofin ƙasarsa bata tsaya kaɗai a ƙasashen dake da albarkatun mai da ma'adinan karkashin ƙasa ba.

Wani kwararre kan diplomasiyyar makamashi a jami'ar Peking Zha Daojiong, ya bayyana cewar manufar Sin itace nunawa ƙasashen Afrika cewar dukkanninsu daidai suke a wajenta .Kuma dangankarsu bata cin moriyar Albarkatun karkashin kasa ce kadai ba.

Sai duk da hakan, ana saran shugaban ƙasar ta Sin da jami'ansa zasu sanar da shiga yarjejeniyoyi na zuba jari da tallafi, a wani abunda ke zama karfafawa tattalin arzikin Afrika gwiwa, a yayinda duniya take fama da matsaloli na tattali.

Magabatan ƙasar ta Sin dai sun tabbatar dacewar tattalin arzikinta zai daɗa bunkasa a wannan shekarar, wanda ke nuna fatan cewar ƙasar ta Sin zata iya ceto wasu kasuwannin dake rugujewa. Priminista Wen Jiabao ya daɗa tabbatar da hakan a wani rangadin aiki daya kai nahiyar turai.

Wen Jiabao Pressekonferenz Brüssel
Priminista Wen JiabaoHoto: AP

Jeffrey Herbst dake koyarwa a jami'ar Miami dake Ohio, yace ƙasashen Afrika guda huɗun da shugaba Hu zai ziyarata, basu da wasu albakatun ƙasa, domin haka ne zasu yi maraba da dukkannin zuba jari da Sin ɗin zatayi a cikinsu.

Shugaba Hu wanda ya sanya dangantaka da ƙasashen Afrika ɗaya daga cikin manufofinsa na ketare, wajibi ne ya tabbatarwa da jami'ansa da ma kamfanonin ƙasar sin ɗin cewar, kutsawa cikin wannan nahiya yana da matukar muhimmanci duk da adawa da suke fuskanta daga gida. Kaza lika dole ne ya tabbatarwa da nahiyar ɗorewar hulɗoɗi na zuba jari da tallafi.

Sai dai wasu ƙwararru kan dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu na ganin cewar, kamfanonin ƙasar ta Sin sun fara janyewa tare da dakatar da wasu ayyuka da suyi a nahiyar.

A 'yan shekarun da suka gabata dai kayayyakin ƙasar Sin sun mamaye kasuwannin nahiyar Afrika, wanda wasu ke dangantawa da kwaɗayin irin ɗumbin albarkatu da Allah ya huwacewa nahiyar.