ZIYARAR SHUGABA SCHÜSSEL NA AUSTRIA A BERLIN | Siyasa | DW | 27.11.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR SHUGABA SCHÜSSEL NA AUSTRIA A BERLIN

Shi dai shugaban gwamnatin kasar Austriya, Wolfgang Schüssel, bai yi amanna da shirin dakatad da hukuncin da aka yi niyyar zatarwa, a kan Jamus da Faransa ba. Matakin da gwamnatocin biranen Berlin da Paris suka dauka, na hana Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai sanya musu takunkumin tsuke lalita, saboda rashin kiyaye ka'idojin kare darajar kudin Euro da suka yi, ya bata wa mahukuntan birnin Vienna rai. Sabili da hakan ne kuwa, Schüssel da kansa, a matsayinsa na shugaban gwamnatin Austriya, ya zo Berlin don bayyana wa Jamus rashin jituwarsa. Bayan tattaunawar da ya yi da shugaba Schröder dai, Schüssel ya yi kira ga Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai da ta yi wa ka'idojin kare darajar kudin Euron kwaskwarima, ta kuma yi la'akari da irin matsalolin da aka samu a yanzu, a duk sauyin da ta ga ya dace a yi wa yarjejeniyar. Duk da nuna bacin ransa ga babakeren da Jamus da Faransa suka yi wa Hukumar Turan wajen zartar da hukunci a kansu dai, shugaban Austriyan ya bayyana cewa, bai ga wata bukatar da akwai ta daukaka kara game da kuri'ar da ministocin kudi na Kungiyar Tarayyar Turai suka jefa don mara wa Faransan da Jamus baya ba. A nasa ganin dai:- "Za a shafe kusan shekaru 2, kafin a warware irin wannan rikicin. Ba za mu iya ta jira ba kuwa, a duk tsawon wannan lokacin. Ina ganin abin da ya kamata mu yi yanzu ne, tuntubar juna, don shawo kan wannan matsalar. Muna bukatar ka'idoji, don kayyade yadda za mu tafiyad harkokinmu cikin kungiyar. Daukaka kara, gurbata yanayin kawai zai yi." Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ma dai ya goyi bayan wannan ra'ayin. A nan ne kuma kawai shugabanin biyu suka amince da ra'ayi daya. A huskar siyasar nahiyar Turai kuwa, da akwai wani gibi mai fadi, tsakanin ra'ayoyinsu. Ita Austriya dai na sha'awar ganin cewa, nan gaba, ko wace kasa za ta sami a kalla jami'i daya a cikin Hukumar kungiyar Hadin Kan Turan. Amma shugaba Schröder, ya fi goyon bayan fasalin da kwamitin shirya daftarin kundin tsarin mulkin Turan ya gabatar, inda bayan an fadada yawan mambobin kungiyar zuwa 25, ba ko wace kasa ce za ta iya samun wakilci a Hukumar ba. Kamar dai yadda ya bayyanar:- "Ban ga wata fa'ida ba, ta nuna alamu kamar bamu da wani bambancin ra'ayi a kan wannan batun ko kuma wasu batutuwa daban. Amma na tabbatar cewa, wadannan bambance-bambance ra'ayoyin ba za su janyo wargajewar tarukanmu ba." Ziyarar da shugaban kasar Austriya ya kawo a nan Jamus dai, shi ne na farko tun shekaru 6 da suka wuce. An dai sami hauhawar tsamari a huldodin dangantaka tsakanin kasashen biyu, saboda goyon bayan da Jamus ta yi, ga takunkumin da Kungiyar Hadin Kan Turan ta sanya wa makwabciyarta Austriya a cikin shekara ta 2000, yayin da jam'iyyar `yan mazan jiya ta ÖVP, ta kafa gwamnatin hadin gwiwa da jam'iyyar FPÖ ta `yan tsageru masu tsatsaurar ra'ayi. Har ila yau dai, shugaba Schüssel na jagorancin gwamnatin hadin gwiwa ne tsakanin jam'iyyarsa ta ÖVP da jam'iyyar FPÖ. Amma an sasanta rikicin da ya janyo saniyar waren da kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai suka yi wa kasarsa.
 • Kwanan wata 27.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnN
 • Kwanan wata 27.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnN