ZIYARAR SHUGABA RAU A TSIBIRIN ZANZIBAR | Siyasa | DW | 23.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR SHUGABA RAU A TSIBIRIN ZANZIBAR

A ziyarar da yake kai wa kasar Tanzaniya, shugaban kasar Jamus Johannes Rau, ya yi bulaguro zuwa tsibirin nan na Zanzibar. Tun 1964 ne wannan tsibirin ya hade da kasar Tanzaniya. Amma har ila yau, ana samun hauhawar tsamari a fagen siyasa, tsakanin mazauna tsibirin da na kasar Tanzaniya.

Shugaba Rau tare da shugaba Benjamin Mkapa na Tanzaniya, a lokacin saukarsa a birnin Dar-Es-Salaam

Shugaba Rau tare da shugaba Benjamin Mkapa na Tanzaniya, a lokacin saukarsa a birnin Dar-Es-Salaam

Wannan ziyarar dai, ita ce ta farko da shugaba Rau ya taba kaiwa a tsibirin na Zanzibar. Bisa tsarin shirin bulaguron dai, shugaba Rau ya taso ne daga birnin Dar-es-Salaam, a cikin jirgin sama, kirar Fokker, na shugaban Tanzaniyan, ya sauka a tsibirin bayan minti 20. Kai tsaye, bayan saukarsa, sai ya wuce zuwa fadar shugaban Zanziban, Amani Karume, inda aka yi masa kyakyawar marhaba. Amma barkewar hadari ba zato ba tsammani, da ruwan saman da aka yi ta yi kamar da bakin kwarya, sun sa an sake shirye-shiryen da aka tsara wa shugaban. Duk da hakan dai, ya dage kan sai ya ziyarci tsohon garin birnin na Zanzibar. Bayan ziyarrar ne ya bayyana cewa:-

"Na yi mamakin ganin turawa masu yawon shakatawa da yawa a nan fiye da wasu wurare. A nawa ganin dai, nan wuri mai gamsad da masu yawon shakatawa. Amma ana bukatar karin yawan gine-gine da kuma inganta wadanda suke nan yanzu, idan ana son Zanzibar din ya yi ta janyo Turawa masu yawon shakatawa."

Akwai dai tsoffin gidajen `yan mulkin mallaka, da kuma dogayen gine-gine a birnin Zanzibar. Wadannan gine-ginen kuwa na bukatar gyara, saboda tun da tsohon shugaban kasar, marigayi Julius Nyerere ya sa aka gina su, ba a taba yi musu gyara ba kuma. A cikin shekarar 1963 ne dai tsibirin na Zanzibar ya sami `yancin kai. A shekarar 1964 ne kuma ya hade da kasar Tanzaniya. Amma duk da haka, ana iya ganin bambanci tsakanin mazauna Tanzaniyan da kuma `yan tsibirin. Shugaba Rau ma ya lura da irin wannan bambancin a lokacin ziyararsa, inda ya bayyana cewa:-

"Ina ganin cewa, mazauna tsibirin na Zanzibar, ba sa sakewa sosai wajen cudanyarsu da sauran `yan kasar baki daya. Ban san dai dalilan da suka janyo hakan ba."

Babu shakka har ila yau ana samun hauhawar tsamari a fagen siyasa, tsakanin `yan tsibirin Zanzibarn da mazauna kasar Tanzainiya. Tsibirin dai na da tsohon tarihi, inda sarakunan kasashen Larabawa suka shafe karnuka suna yi masa mulki. Har ila yau kuma, akwai angizonsu a nan. Mafi yawan `yan tsibirin dai musulmi ne, kuma ko wane maziyarci, zai ga alamun haka a zahiri a halin rayuwar mazaunan.

A ziyarar da ya kai a tsibirin, shugaba Rau ya nuna gamsuwarsa da tattaunawar da ya yi da shugaba Karume. Shugaban na Zanzibar dai, inji Rau, ya yi kira ne ga Jamus, ta ta kara maido da hankalinta wajen taimakar Tanzaniya. Ya kuma nuna bacin ransa da ganin yadda kasashen Turai ke nuna rashin sha’awa kann tsibirin. Sabili da haka ne ya yi kira ga Jamus da ta jagoranci daukar matakin sake wannan halin.

 • Kwanan wata 23.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvl9
 • Kwanan wata 23.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvl9