Ziyarar Shugaba Bush Ga Nahiyar Turai | Siyasa | DW | 21.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Shugaba Bush Ga Nahiyar Turai

A yau litinin ne shugaban kasar Amurka George W. Bush ya fara wata ziyara ta yini biyar ga kasashen Turai

Shugaba Bush da P/M Guy Verhofstadt na Belgium

Shugaba Bush da P/M Guy Verhofstadt na Belgium

Tun kafin tashinsa daga birnin Washington, shugaba George W. Bush ya bayyana wa ‚yan jaridar dake rufa masa baya manufar wannan ziyara tasa, inda ya lashi takobin yin bakin kokarinsa wajen kyautata yanayin dangantaku tsakanin Amurka da kawayenta na nahiyar Turai. A lokaci guda, fadar mulki ta White House ta buga wani bangare na jawabin da aka shirya shugaba Bush zai gabatar ga jami’an diplomasiyyar kasashen Turai da zasu halarci zauren da zai gabatar da jawabin nasa. A cikin jawabin dai kamar yadda aka tsara shugaba Bush zai yi batu a game da shiga wani sabon babi ga dangantakar kasashen kawancen tsaron NATO. Akwai bukatar karfafa hadin kai tsakanin sassan biyu bisa manufar yada ‚yanci da walwala a duk fadin duniya. Shugaban na Amurka na neman hadin kai daga kasashen turai, wadanda a zamanin baya suka bayyana adawarsu da mamayar iraki, domin kare makomar jaririyar demokradiyyar da aka dasa tubalinta a kasar ta Larabawa. Ba shakka irin wadannan bayanai na neman sulhu abu ne da zai dadada wa kasashen na Turai. Za dai a gudanar da liyafar cin abincin dare tsakanin shugaba Bush da Jacques Chirac na Faransa, wanda ke daya daga cikin masu sukan lamirin manufofin Amurka dangane da Iraki da kakkausan harshe. A kuma jibi laraba zasu gana da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder, wanda shi ma ya fito fili ya bayyana adawarsa da matakin yakin Irakin. A jawabin da zai gabatar dai kamar yadda aka samu bayani, shugaba George W. Bush zai nemi hadin kan kasashen Turai a fafutukar neman zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinawa. Sai dai har yau akwai sabanin tsakanin Amurkan da kasashen Turai dangane da manufofin Iran da Siriya da kuma China. Manazarta sun hakikance cewar ba za a tabo wannan batu ba sai bayan da shugaba Bush ya kammala ziyarar tasa ta yini biyar ga kasashen Turai. Kasashen Amurka da Faransa sun zayyana wani kudurin da zasu gabatar wa da kwamitin sulhu na MDD wanda ya tanadi janyewar sojojin Siriya daga Lebanon. A nasu bangaren ministocin harkokin wajen kasashen KTT, wadanda aka shirya zasu sadu da shugaba Bush a yau litinin a birnin na Brussels sun tsayar da shawarar bude wata cibiya a birnin Bagadaza, wacce zata rika hada kan matakan ba da horo da ilimantarwa ga alkalan Iraki da kuma jami’an ‚yan sandan kasar. A lokacin wani dan gajeren taron kolin da zasu gudanar a gobe talata, shugabannin kasashen kungiyar zasu gabatarwa da shugaba Bush takardar shawarar. Kazalika a gobe talata din an shirya taron kolin kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO, inda ake sa ran halartar P/M kasar Ukrain Viktor Yuschetschenko, wanda ke bakin kokarinsa wajen ganin kasarsa ta samu karbuwa a KTT.