1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaba Bush a Yankin Gabas ta Tsakiya

Sani, IbrahimJanuary 9, 2008

Ziyarar Mr Bush a Yankin Gabas ta Tsakiya, a kokarin shawo kan rikicin da yankin ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/CmTp
Shugaba Bush da Mr Olmert da kuma Mr Mahmud AbbasHoto: AP

Shugaba Bush na Amirka ya nufi Yankin Gabas Ta Tsakiya, don fara wata ziyarar aiki, a kokarin shawo kan rikicin dake tsakanin Israela da kuma Yankin Falasdinawa. Da farko dai an shirya cewa Mr Bush zai yada zango ne a Israela don tattaunawa da Faraminista Ehud Olmert da kuma shugaban Kasar Mr Shimon Peres, a gobe Laraba idan Allah ya kaimu.Ziyarar ta Mr Bush tazo ne a dai-dai lokacin da magoya bayan Jam´iyyar Fatah da ´yan kungiyyar Hamas ke ci gaba da arangama da juna a zirin Gaza. Hakan dai a cewar rahotanni ka iya mayar da hannun agogo baya, game da burin da aka sa a gaba na warware rikicin da yankin ke fuskanta. Kafafen yada labarai sun rawaito shugaban na Amirka Mr Bush na na jaddada muhimmancin samo bakin zaren warware rikicin na Yankin Gabas Ta Tsakiya, jim kadan kafin tashinsa izuwa Yankin Na Gabas Ta tSakiya.

´´ Mr Bush ya ce wannan babban aikine, domin yana bukatar daukar ingantattun matakai, to amma duk da haka ina cike da fatan cewa za a samu cimma maslaha. Amirka zata ci gaba da kokari na ganin bangarorin dake rikici da juna, wato Israela da Yankin Falasdinawa sun kasance makotan juna cikin yanayi na zaman lafiya´´

Mr Bush, wanda ya taba ziyartar Israela lokacin yana Gwamnan jihar Texas, ya tabbatar da cewa a wannan karo zai yi amfani da wannan damar, wajen ganin bangarorin biyu sun ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar sulhun da aka cimma a lokacin taron birnin Annapolis, na ganin cewa an samar da ´yan tacciyar Kasar Falasdinu a cikin wannan shekara ta 2008. A waje daya kuma a yayin da Mr Bush ke ci gaba da dakon ganin an cimma wannan buri da aka sa a gaba, Mr Jirbawi, daya fito daga Yankin na Falasdinawa na ganin cewa matukar Israela bata canza matakin da take a kai yanzu ba, to babu shakka akwai sauran tsalle a gaba.

´´ Mr Jirbawi ya ce ba zamu taba yarda aci gaba da yaudararmu ba, domin Israela ta ce ta dakatar da shirin ci gaba da gine-gine a matsugunan Falasdinawa, to amma har yanzu wannan al´amari na ci gaba da wanzuwa. A hannu daya kuma ga mamaye da sojin Kasar ke ci gaba da kaiwa a kullum ranar Allah ta´ala, zamu yarda da wannan shiri na sulhu ne kawai idan mun ga canji daga bangaren Israela´´

A yanzu haka dai da yawa daga cikin masu nazarin harkokin siyasar yankin na Gabas Ta Tsakiya, na zargin Mr Bush da yin shakulatin bangaro da rikicin yankin a tsawon shekaru bakwai na mulkinsa.To amma a cewar da yawa daga cikinsu, wannan ziyara da shugaban zai fara a gobe, alama ce dake nu ni cewa shugaban da gaske yake wajen shawo kan wannan rikici.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, ziyarar ta Mr Bush tazo ne a dai dai lokacin da Faraminista Ehud Olmert na Israela da kuma takwaransa na Falasdinawa Mahmud Abbas ke ganawa a jerusselem, a kokarin cimma wani tudun dafawa, dangane da shawo kan rikicin dake tsakanin bangarorin biyu. Ana sa ran shuwagabannin zasu yi waiwaye ne adon tafiya, dangane da tattaunawar sulhun data gudana a birnin Annapolis, a watan Nuwambar bara dangane da warware wannan rikici na Yankin Gabas Ta tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da kuma yankin na Falasdinawa.