Ziyarar shugaba Bush a Indonesia | Labarai | DW | 20.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaba Bush a Indonesia

Shugaba George W Bush na Amurka ya samu kyakkyawan maraba daga shugaban kasar Indonesia,a fadar sarautar zamanin mulkin mallaka na garin Bogor,adaidai lokacinda masu bore a wasu sassan birnin ke Ihun Allah wadan Shugaba Bush.Indonesia dake zama kasar datafi kowace yawan alummar musulmi a duniya ,na mai kasancewa daya daga cikin kasashe dake marawa Amurka baya,a harkokin yakar taaddanci a wannan yanki,duk dacewa Gwamnatin da mafi yawan yan Indonesian na adawa da manufofin Amurka a yankin gabas ta tsakiya.Shugaban na Amurka wanda ya ke matakin karshen ziyararsa a yankin Asia,yayi hannu da shugaba Susilo BambangYudhoyono,kafin su fara wata ganawa ta saoi 6,inda ya bayyana alfaharinsa da Indonesi.