Ziyarar shugaba Bush a Albaniya | Labarai | DW | 10.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaba Bush a Albaniya

A wata gejeriyar ziyara ta farko da ya kaiwa Albaniya shugaban Amirka GWB ya gana da FM Sali Berisha. A wannan ziyara ta sa´o´i 7 Bush zai kuma gana da shugaba Alfred Moisiu a Tirana babban birnin Albaniya. Sabanin ziyarar da ya kai a Italiya, Bush ya samu kyakkyawar taraba lokacin da ya isa a birnin Tirana. A wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da FM Berisha, Bush ya nuna farin cikinsa da wannan ziyara.

“Ina alfahari da na zama shugaban Amirka na farko dake kan kujera da ya kaiwo ziyara a Albaniya. Babbar karramawa ce in wakilci kasa ta a nan. Na dade ina begen wannan rana da ni da mai daki na. Dalili kuwa shine ina sha´awar zuwa kasashen dake aiki tukuru don kafa hukumomi na demukiradiyya.”