1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR SCHRODER A AMURKA

ZAINAB AM ABUBAKAR.February 27, 2004
https://p.dw.com/p/Bvle
Shugaba George W Bush na Amurka ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Gehard Schroder a fadar gwamnatin Amurka ta white House.Shugaban na Amurka bai boye bacin ransa dangane da matsayin da Jamus ta dauka kann yakin kasar Iraki ba na nuna adawa da hakan.

Bayan ganawan sirri na shugaban biyu,tare da bayyana a gaban jamaa anasaran shugabanin biyu zasu bada sanarwar dake tabbatar da ingantuwan dangantaka tsakaninsu.Kakakin Bush Scott McClellan ya fadawa manema labaru cewa Jamus ta kasance babbar kasa dake bawa Amurka cikakken goyon baya wajen yaki da ayyukan yan taadda,tare da yunkurin kasashen keyi na tabbatar tsaro a nahiyar turai.

To sai dai babu tabbacin samun nasaran wannan ziyara ta shugaban gwamnatin Jamus a fadar gwamnatin na Amurka a karo na farko cikin shekaru biyu da suka gabata,musamman ma a dangane da batun tattalin arziki da ake saran shugabanin biyu zasu tattauna.Kakakin White House ya bayyana cewa har yanzu babu tabbaccen mataki dangane da matsayin da Amurka ta dauka kann hana masanaantun kasashen da sukayi adawa da Irakin kwangilan ginin kasar.

Jamus dai na kann bakanta na kin bada gudummowasn sojojinta zuwa kasar Iraki,koda a bangaren kungiyar tsaro ta NATO ne.To sai dai jamian gwamnatin Amurkan sun sanar dacewa sabanin dake tsakanin Amurka da Jamus ya zamanto tarihi domin sun cimma daidaito. Bugu da kari sun yabawa kokarin Schroder wajen fitowa fili karara tare da nuna goyon bayansa wa gudummowan shugaba Bush wajen warware rikicin yankin gabas ta tsakiya.To sai dai manazarta sunce ba fatar baka kadai ba,kamata yayi aga ingantuwan wannan dangantaka tsakanin Jamus da Amurka a zahiri,musamman ma dangantakar euro da Dala.

Shugaban na Amurka dai na dada karfafa matakan kampaign na neman zarcewa kann mukamin nasa,inda yake kokarin kalubalantar zargi da sauran abokan adawa daga jammiyar Democrats keyi,wanda ake ganin cewa ziyarar na shugaban gwamnatin Jamus zai taimaka masa nesa ba kusa ba.Daga yanzu zuwa watan Yuli ana saran Bush zai gana da shugabanin turai masu arzikin masanaantu da ake kira G8,kana shugabanin kungiyar tarayyar Turai EU a taron da zasu gudanar a Ireland.Kana mai yiwuwa zai halarci taron kungiyar tsaro ta NATO da zai gudana a Turkiyya a karshen watan Yuni.