Ziyarar Schröder ga Amurka | Siyasa | DW | 27.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Schröder ga Amurka

A yau litinin shugaban gwamnatin Jamus G. schröder zai gana da shugaba G.W.Bush na Amurka a birnin Washington

Schröder akan hanyarsa zuwa Washington

Schröder akan hanyarsa zuwa Washington

Tun bayan balaguron da shugaba George W. Bush na Amurka ya kawo wa kasashen Turai a cikin watan fabarairun da ya gabata huldar dangantaku ta fara daidaituwa tsakanin Jamus da Amurka. A duk lokacin da wata dama ta samu a gare shi, shugaba George W. Bush ba ya wata-wata wajen yaba wa Jamus, musamman dangane da rawar da take takawa a kai ruwa-ranar da ake yi a game da shirin makamashin nukiliya na kasar Iran. Kazalika shugaban na Amurka ya fito fili ya bayyana fatansa na tabbatar da hadin kann kasashen Turai, bayan da kasashen Faransa da Netherlands suka yi fatali da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen KTT. Ko shakka babu kuwa a game da cewar tattaunawar tasu ta yau litinin zata gudanar ne karkashin wani kyakkyawan yanayi na zumunci da kawance daidai da yadda lamarin ya kasance shekarar da ta gabata lokacin da Schröder ya kai wa Bush ziyara, inda shugaban Amurkan ke cewar:

Akwai kakkarfan hadin kai tsakaninmu a kokarinmu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyr hankali a dukkan sassa na duniya. Wannan ziyarar da ka kawo mana, babbar girmamawa ce a gare ni, ina maka marhabin lale.

To sai dai kuma duk da haka tana kasa tana dabo dangane da dangantakar gwamnatin Amurka da ta SPD da The Greens a nan Jamus. A makon da ya gabata ministan tsaron Jamus Peter Struck ya soke wata ziyarar da ya kuduri niyyar kaiwa kasar Amurka, saboda takwaransa sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya gayyade masa ganawa ce ta gajeren lokaci, ganin cewar Jamus har yau ta ki ta tura sojojinta domin rufa wa sojan Amurka baya a mawuyacin halin da suke ciki a Iraki. Michael O’Hanlon daga cibiyar nazarin al’amuran siyasa ta Brookings Institution yayi bayani game da haka yana mai cewar:

Sojojinmu na cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi a kasar Iraki. Kasashen Jamus da Faransa na da cikakken ikon taimaka mana in har suna sha’awar yin hakan. Amma mu kanmu mun san wannan maganar ba ta taso ba. A sabili da haka shugaba Bush ba zai tabo wannan maganar a ganawarsa da Schröder ba, duk da bukatar taimakon da muke yi ruwa a jallo.

Mai yiwuwa a sakamakon kyamar yakin Irakin da Jamus ke yi ne, ita kuma Amurka a nata bangaren ta ki ta fito fili ta ba wa kasar Goyan baya a fafutukarta ta neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD.