1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Sarkozy a Libya

July 25, 2007

Ziyarar shugaban faransa a Tripoli

https://p.dw.com/p/Btuw
Shugaba Nicholas Sarkozy
Shugaba Nicholas SarkozyHoto: picture alliance/dpa

Acigaba da kokarin inganta dangantakar siyasa da kasuwanci da kasar Libya mai albarkatun man Petur,ayau ne shugaba Nicholas Sarkozy na kasar Faransa ya kai ziyara Tripoli,bayan taimakawa wajen sakin jamian kiwon lafiyan ketaren nan guda shida.

Wannan ziyara ta Shugaban na faransa tazo ne yini guda bayan Libyan ta sallami jamian kiwon lafiyan guda shida,sakamakon cimma yarjejeniyar kawance na kasuwanci da kungiyar tarayyar turai.

Jamian shida da suka hadar Nas Nas na Bulgaria 5 da likitan palasdinu guda dai sun bar Tripoli ne da jirgin saman kasar faransa,tare da rakiyan uwargidan shugaban Faransan da Commissionar inganta danganta ketare na turai BenitaFerrero-Waldner,bayan kasancewarsu a gidan kurkuku na tsawon shekaru 8,sakamakon sanyawa yara sama da 400 kwayoyin cutar Aids.

Sakin wadannan jamian kiwon lafiya dai shine ya share fagen wannan ziyara da shugaban na faransa kasar ta Libya ayau.

Shugaba Sarkozy yace yana kokarin taimakawa Libya ne komowa cikin dangantakar kasashe ,bayan mayar da ita saniyar ware na sama da shekaru 30 da suka gabata,sakamakon zargin da kasashen yammaci suke wa Libyan na marawa yan tarzoma baya.

A wannan ziyara tasa bugu da kari,shugaban na faransa zai inganda harkokin kasuwanci da Libyan,tare da fadada dangantakar diplomasiyya ta kasarsa da sauran kasashen nahiyar Afrika.

Ministar harkokin tattalin arziki na kasar ta Faransa Christine Lagarde ta bayyana cewa babu gudu babu jada baya a wannan kokarin fadada dangantakar ciniki da Libya…

“Libya itace kasa ta farko data zabi faransa,domin saukaka biyan kudin haraji,adangane da shigi da ficen hajjoji,saboda haka Zamu bunkasa dangantakar cikikayya da wannan kasa”

Shugaban na faransa dai ya taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma yarjejeniyar ganin cewa an saki wadeannan jamian kiwon lafiyan na kasashen ketare daga kasar ta Libgya.

“Sakorzy yace nida shugaban hukumar gudanarwa na turai Barroso,munyi iyakar kokarimmu adangane da wannan rikici mai sarkakkiyar gaske,kuma ta hanyar aiki kafada da kafrda ne muka cimma nasara.Kuma dole ne a tallafa Libya sake komowa da ita cikin sauran kasashen duniya,bayan saniyar ware da aka mayar da ita a baya”

Dangantaka tsakanin faransa da Libya ya lalace ,sakamakon harin da aka kaiwa jirgin faransa a 1989.Faransan dai a wancan lokacin ta zartar da hukunci akan yan Libya guda 6,ba tare da sun bayyana ba,amma Tripoli ta karyata hannu a wannan harin.An samu ingantuwan dangantaka,asakamakon dage takunkumi da kasashen yammaci sukayi daga kan Libya a 2003,domin tayi watsi da makaman kare dangi.