Ziyarar Sarkozy a biranen Mosko da Tiflisi | Siyasa | DW | 09.09.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Sarkozy a biranen Mosko da Tiflisi

Rasha ta amince za ta janye dakarunta daga ƙasar Jojiya

default

Medvedev da Sarkozy da kuma Barroso a Mosko

A ci-gaba da neman hanyoyin diplomasiya don warware rikicin yankin Kaukasian a jiya shugaban Faransa Nikolas Sarkozy wanda kuma shi ne shugaban tarayyar Turai ya yi tattaki zuwa biranen Mosko da Tiflisi. Rasha dai ta ba da tabbacin cewa zata janye dakarun ta daga yankin Jojiya cikin wata guda. A na ta ɓangaren gwamnatin Jojiya ta yi maraba da sakamakon wannan sabon yunƙurin, inda ta yi fata Rasha za ta cika alƙawarin da ta ɗauka.


A wata sanarwa da ya bayar yau shugaban Jojiya Mikahil Saakashvili yayi lale marhabin da labarin dake cewa Rasha ta amince za ta janye dakarunta daga dukkan yankunan Jojiya in ban da yankunan biyu na ´yan aware da cewa wani mataki akan turbar da ta dace.


To sai dai Saakashvili ya dage cewa duk wani shirin warware rikicin na dogon lokaci dole ne ya girmama ´yancin ƙasarsa ciki har da yankunan Ossetia ta Kudu da kuma Abchasia. Da farko bayan tattaunawar da yayi da jagoran tawagar tarayyar Turai kuma shugaban Faransa Nikolas Sarkozy, shugaban Rasha Demitri Medvedev ya yi alƙawarin janye dakarunsa daga Jojiya in ban da yankunan biyu na ´yan aware.


Masu shiga tsakanin na ƙungiyar tarayyar Turai wato Sarkozy da Barroso da kuma Solana sun nuna bajimta da haƙuri. Bayan shawarwarin da suka yi a birnin Mosko jami´an sun je birnin Tifilis cikin dare ɗauke da wannan saƙo daga Mosko. A taron manema labaru an jiyo Sarkozy yana mai cewa.


Ya ce: "Ko da yake ba mu kai gaci ba amma muna samun ci-gaba sannun a hankali. A baya mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, sannan a wannan karon Rasha za ta janye dakarunta daga fagen fama."


Sarkozy ya ce ƙungiyar EU za ta sa ido don ganin Rasha ta aiwatar da yarjejeniyar ta jiya Litinin. Rasha ta ce za ta janye da zarar dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa ciki har da jami´an sa ido 200 na EU sun karɓi ragamar yankin da aka hana aikin soji a ciki.


Yanzu haka dai wani babban taron ƙasashen duniya da zai gudana a birnin Geneva zai share fagen tattaunawar samar da zaman lafiya, musamman dangane da batun matsayin yankunan biyu na ´yan aware da ƙasashen duniya ba su amince da su ba.


A na sa ɓangaren shugaban Jojiya Saakashvili ya fi damuwa game da haɗin kan ƙasar inda ya ce za su yi amfani da hanyoyin lumana don cimma manufar da aka sa gaba.


Ya ce: "Ina jin a daren yau mun samu ɗan ci-gaba. Yanzu haka dai mun kusanci matakin aiwatar da shirin nan mai rukunai shida wanda shugaba Sarkozy ya tsara."


A halin da ake ciki ƙungiyar tarayyar Turai da sauran ƙasashen duniya sun nuna gamsuwa da wannan ci-gaba da aka samu inda suka yi kira ga hukumomin birnin Mosko da su cika alƙawarin da suka ɗauka domin kawo ƙarshen zubar da jini a yankin na Kaukasian.