Ziyarar Sarkozy a ƙasar Amirka | Labarai | DW | 08.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Sarkozy a ƙasar Amirka

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kammala ziyarar aiki da ya kai ƙasar Amirka don ƙarfafa dangantaka da haɗin kai a kan batutuwa na ƙasa da ƙasa. Shugaban wanda ya sami kyakyawar tarba dake nuna cewa ƙasashen biyu na muradin dinke ɓarakar da ta samu a tsakanin su a game da yakin Iraqi a zamanin tsohon shugaban Faransa Jacque Chirac. A jawabin da ya yiwa majalisar dokokin Amurka, Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya tabbatar musu cewa ƙasar sa za ta tsaya tsayin daka tare da haɗin gwiwa da Washington wajen ganin Iran bata kai ga mallakar makamin ƙare dangi ba da kuma yaƙi da ayyukan taáddanci a Afghanistan. Shugabanin biyu sun kuma tattauna a game da batun Iraqi da yankin Gabas ta Tsakiya.