1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Sarki Abdalla Ga Girka

December 21, 2005
https://p.dw.com/p/BvFZ

Jordan/Greece

Sarki Abdallah na Jordan ya sauka a kasar Girka a wata ziyarar aiki ta kwana biyu da zai yi akasar,inda ministocin sa da suke rufa masa baya zasu sanya hannu a yarjejeniyoyin da suka jibanci kasuwanci da harkokin yawon buda idanu tsakanin kasashen biyun.

Bayan da ya isa kasar sarkin ya gana shugaban Girkan Karolos Papoulias,kuma a yayin ziyarar zai gana da Pm Costas Caramanlis da shugabannin jamiyyar adawa da masu masanaantu na kasar da kuma magajin garin Athens Dora Bakoyannis.

Uwar gidan sarkin na jordan sarauniya Rania da ministan kasuwanci tare da ministan harkokin ,waje da kuma magajin garin Amman na daga cikin masu rufawa sarkin baya a ziyarar.

Kasar Girka wacca yar kungiyar gamayyar turai bisa alada tanada alaka ta kut dakut da kasashen larabawa.

Israel Palast

Hukumomin Israela sunce zasu haramtawa palasdiwan dake zaune a yankin data mamaye ba na gabashin birnin Jerusalem su shiga zaben yanmajalisar da za ayi ba awatan Janairu .na shekara mai kamawa ba,abinda ya haifar da wani mummunan suka na cewa tana dai son ta gurgunta zabenne kawai.

An ruwaito wani jamiin gwamnatin Israelan da ya bukaci a sakaya ,sunansa yana cewa a baya israela ta bari Palaskdiwan dake yankin sun kada kuriunsu a gidajen waya amma a wannan karan sam sam hakan bazai yiwuba.

Jamiin yace bazasu bari wani abu na siyasa ya gudana a yankin ba musammam ma tunda Hamas tana cikin zaben,kuma zasuyi duk abinda zasu iya su kare birnin na ,Jerusalem wanada ya kira babban birninsu daga hare hare.

Kimanin palasdinawa dubu dari biyu ne dai ke zaune a wannan yanki na gabashin jerusalem wanda Israelan take rike dashi tun loacinda ta kwaceshi a yakin da tayi da larabawa a alif dari tara da sittin da bakwai,amma har yanzu kasashen duniya suna sanya yankin a cikin daya daga cikin wuraren palasdinawa da Israelan ta mamaye.

Saudi/GB

Nan bada .jimawa bane Kasar Saudi Arabia take saran kammala wata yarjejeniya akan sayen jiragen soji na zamani tsakaninta da Birtaniya.

Ministan tsaro na Saudiyan yarima sultan bin Abdul aziz ,ya shedawa manema labarai h jin kadan bayan ganawarsa da takwaran sa na birtaniya John Reid wanda ke ziyara a kasar.

Kafofin kusa da mahukuntan ,saudiyan sunce tatttaunawar ta kunshi sayen kusan jirakgen 48 da kuma .ake saran akwai zabin idan saudiyan tana bukata Birtaniyan zata iya sayar mata har zuwa 72 ma.

Sai dai ba a bayyana kudin sayen jiragen ba,amma editan wata mujalla data shafi harkokin tsaro dake London francis Tusa yace jirgin sanfurin euro fighter typoon akalla kowana daya yakan kai pam miliyan 65 hade da makaman sa da horadda masu sarrrafa shi da kuma sauran abebadai.

UN/Com

Majalisar dinkin duniya ta kafa wata sabuwar hukuma ta tabbatar da zaman lalfiya domin taimakawa kasashen da suka far fado daga rikice rikice musamman ma na Afrika da kada su sake fadawa cikin rigingimu.

Hakan dai yana daga ,cikin manyan sauye sauyen da shugabannin kasashen duniya suka amince akai ne a babban taron majalisar da akayi awatan satumba.

Kwamitin tsaro na majalisar mai mutane 15 da kuma babban taron majalisar mai kasashe 191 sune ska amince da kafa hukumar ta dun dun dun.

Babban sakataren majalisar Kofi Annan yace burin kafa hukumar shine domin a wani saban tsari daya dace daga ire iren faman da majalisar tayi na kare rikice rikice da tabbatar da zaman lafiya da kiya ye yanci dan adam da tabbatar da doka akan kowa da kuma ayyukan jin kai

Iran /Nuclear

Kasar Iran ta kara jaddada aniyarta taci gaba dasamar maaikatar ta nukilya a tattaunawar da takeyi da masu shiga tsakani daga kasasöhen jamus da faransa da kuma ingila a birnin vienna na –Austria.

Wakilan kasshen turai a taron sunce ganawar tasu da iran din basa ganin zata hana iran cigaba da shirin nata duk kuwa da hadarin mika ta ga kwamitin tsaro na MDD dake tattare da kafewar da take cigaba dayi.

Taron na vienna shine na farko tun .watan a.gusta bayanda Ioran din tace zata ci gaba da shirin nata na nukiliya wanda ta kasfe dacewa na .samar da makamashi ne amma ba makamai ba.

NGR/OIL

Wadansu yanbindiga da ba asan ko suwanene ba sun kai harin nakiya akan wani butun mai a yankin da ake hako mai na Naija Delta dake Najeriya.

Harin wanda aka kai akan bututun mai da kamfanin hakar mai na Shell yake amfani dashi ya haifar da kwararar mai mai yawan gaske ya kuma tayar da wuta ganga ganga,sannan yayi sanadiyyar mutuwar mutane takwas,ya kuma rage yawan man da kamfanin yake samarwa a kullum da kusan ganga dubu dari da sabain.

Har kawo yanzu dai maaikatan mai suna can suna kokarin shawo kan wutar dake ci har yanzu.

Kafofin dake kusa da kamfanin na Shell suna largin cewa harin yanada alaka da siyasa ta cire tshohon gwamanan Bayelsa Mr Daprie Alamieseigha.

Saddam/

A yaune aka cigaba da sauraran shariar tshohon shugaban Iraki saddam Hussaini da mukarraban gwamnatisa bakwai akan zargin kashe mutane dari da arbain da takwas a garin Dujail a lokacin mulkinsa.

A zaman .na yau mutumin da ya bada bahasi ya bayyana .a fili ba kamar a baya bainda masu bada bahasin suka rinka magana da bayan labule.

Mai bada bahasin wanda ya bayyana sunan da Ali Hassan Al Haidari wanda yake dan shekara goma sha hudu a lokacinda abin ya faru, ya shedawa kotun yanda aka kashe dan uwansa da kuma yanda aka ganawa wasu azaba.

A lokacinda kotun take zamannata Saddam ya bukaci da a dakatar da zamandomin ayi sallar azahar amma alkalin yaki amincewa da hakan wanda hakan yasa Saddam din ya dauki tsawon minti goma yana sallar a kan kujerarsa.