Ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka a gabas ta tsakiya

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta tsawaita ziyarar da take yi a kasar Israila domin samun damar cimma masalaha tsakanin mahukuntan Israilan dana Palasdinawa don sake bude kann iyakar Gaza da kasar Masar. Mashawarta na ta kokarin samar da wata yarjejeniya don baiwa Palasdinawa damar shige da fice ta kann iyakar ba tare da tsangwama ba. Hakan kuwa ya biyo bayan janyewar Israilan ne daga yankin na Gaza. Hukumomin Palasdinawa sun baiyana bude kan iyakar da cewa yana muhimmanci ga bunkasar tattalin arzikin alúmomin yankin.