Ziyarar sakataren Burtaniya a Pakistan | Labarai | DW | 26.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar sakataren Burtaniya a Pakistan

Sabon sakataren harkokin wajen Burtaniya David miliband ya tattauna da shugaban kasar Pakistan Parvez Musharraf a babban birnin kasar Islamabad.Bayan ganawar tasu Miliband ya baiyana cewa Burtaniya tana da burin ganin an samu zaman lafiya a Pakistan tare kuma da kokarin Musharraf wajen dakile harkokin wadanda suke da alaka da kungiyoyin Taliban da Al Qaeda.

Ziyarar ta Miliband a Afghanistan da Pakistan tazo ne a daidai lokacinda Musharraf yake kokarin kare mulkinsa bayan sabani da aka samu game da batun korar babban alkalin alkalan kasar da kuma farmaki da sojojinsa suka kai kann wani masallaci a Islamabad,wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 70.