Ziyarar Rumsfeld a Iraq | Siyasa | DW | 12.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Rumsfeld a Iraq

Rumsfeld ya isa Iraki ne kwana guda bayan yan kunar bakin bakin wake sun kashe mutane 26 a bakin kofar shiga yankin tsaro da aka kebe na gwamnati.

default

Rumsfeld ya gana da shugabanin gwamnatin Iraqi,bayan da babban komandan sojin Amurka a Iraqi ya sanar masa da cewa,dakarun yan shia suna kara hura wutar zubda jinni a kasar.

Jim kadan dai bayan isar Rumsfeld birnin Bagadaza a yau din,said a wani dan kunar bakin wake ya shiga wani gidan saida abinci inda ya halaka kansa da kuma wasu mutane 7,hakazalika jamian tsaro sun gano gawarwakin wasu direbobin bus bus da aka sace tun farko a arewacin Bagadaza.

Sakataren tsaron na Amurka ya fadawa manema labari cewa,yanzu ana cikin wani yanayi wadda cewa,samun kyakyawar tsaro ya dogara ne akan shirin sasanta tsakani da kuma inganta maaikatun gwamnatin kasar ta Iraqi.

Batun tsaro shine ke kan gaba a tattaunawar Rumsfeld da komandojin sojin Amurka dake Iraqi.

Tashe tashen hakula dai sai kara ci gaba sukeyi a birnin Bagadaza,duk kuwa da dauki da dubban sojoji suke kaiwa cikin birnin.

Mutane da dama dai sun rasa rayukansu a birnin na Bagadaz,cikin hare hare mafiya muni na baya bayan nan.

A garin Balad,Rumsfeld ya baiyanawa sojojin cewa,bat a hayar soji ne kadai zaa iya magance matsalar tashe tashen hankula a Iraqi,yace babban abu shine a hada kai da yan sunni,dake tsakanin mafi yawa na shia a kasar ta Iraqi.

Game da batun rage sojin Amurka a Iraqi kuwa,Rumsfeld yace,har yanzu basu kai ga wannan batu ba,yana mai cewa,dole ne komandojin Amurka da jamian Iraqi su gana domin yi nazarin bukatun da ake da su,na sojin Amurkan kafin a fara batun rage yawansu.

Yanzu haka dai Amurka tana da sojoji 129,000 a Iraqin fiye da shekaru 3,wadanda cikinsu kimanin 2,5000 suka rasa rayukansu.

Tunda farko dai shugaba Bush na Amurka,yace dakarun Amurka zasu kasance a Iraqin,har sai abubuwa sun daidaita,hakazalika Rumsfeld ya bukaci janar Casey da kuma jakadan amurka a Iraqi da suyi aiki tare da gwamnatin Iraqin domin samo sahihiyar hanya da ta dace kuma ta karbu ga bangarorin biyu.

Baya ga batun tsaro a Bagadaza sai kuma batun hade jamian soji dana yan sandan Iraqi cikin tattaunawar tasu.

Sai dai yace ba zai tatauna game da zargin da akeyiwa wasu sojin Amurka na kashe farar hula na Iraqi,wadanda suka hada da kashe farar hula 24 a Haditha da kuma yin fyade da kashe wata budurwa da iyayenta,batu da ya sake yada martabar Amurka a idanun duniya.

Wannan batu kuwa ya janyo jamian Iraqi suka dora ayar tambaya akan kariya da sojan Amurka suke da shi daga dokokin Iraqi.

A halin yanzu dai firaminista Nouri al-Maliki,ya bada umurnin bincike cikin batun fyaden da kashe kashen na mahmudiya,amma Rumsfeld yace jamian sojin Amurka zasu dauki mataki akan wannan alamari.

 • Kwanan wata 12.07.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzD
 • Kwanan wata 12.07.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzD