Ziyarar Rumsfeld a birnin Kabul na Afghanistan | Labarai | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Rumsfeld a birnin Kabul na Afghanistan

A dangane da karuwar hare haren da mayakan Taliban ke kaiwa a Afghanistan, sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld ya yiwa kasar ta Afghanistan alkawarin ba ta karin taimako. Da sanyin safiyar yau Rumsfeld ya kai wata ziyarar ba zata a birnin Kabul. Bayan ganawar da yayi da shugaba Hamid Karzai mista Rumsfeld ya jaddada cewar shirin rage yawan dakarun Amirka a kasar da mika ragamar aikin soji ga kungiyar tsaro ta NATO a yankunan da aka fi fama da rikici na kudancin kasar, ba ya nufin Washington ta zame hannunta daga harkokin wannan kasa. Shugaba Karzai ya nunar da cewa raunin rundunar ´yan sandan kasar shi ne musabbabin karuwar ta´addanci a cikin kasar. A wani sabon farmakin da dakarun kawance da kuma sojojin Afghanistan suka kai a lardin Helmand sun halaka akalla mayakan Taliban 30.