Ziyarar Rice da Gates a gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 30.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Rice da Gates a gabas ta tsakiya

Shugaban kasar Amurka ya tura manyan jamiansa biyu Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice da sakataren harkokin tsaron kasar Robert Gates zuwa yankin gabas ta tsakiya domin neman goyon bayan larabawa kann batun Iraqi,haka zalika zasu tattauna batun sayarda makamai ga kawayen Amurka a yankin.

Condoleeza Rice

Condoleeza Rice

Cikin kiraye kiraye da akeyi a cikin gida na janyewar dakarun Amurka daga Iraqi,ana sa ran Rice da Gates zasu kara jaddada sadaukarwar Amurka kann tsaron yankin daga abinda ta kira barazana daga Iran da shirinta na nukiliya.

Bugu da kari kuma gwamnatin Amurkan zata baiyana damuwarta cewa wasu kasashe larabawa yan sunni suna bada taimakon kudi ga mayakan kasashen ketare domin su yaki gwamnatin yan shia’a dake da goyon bayan Amurka a Iraqi.

Koda a karshen mako jakadan Amurka a MDD Zalmay Khalilzad yayi korafin cewa wasu kasashe makwabtan Iraqi ciki har da kasar Saudiya suna yin zagon kasa ga kokarin da akeyi ba wanzar da zaman lafiya a Iraqi.

Baya ga kasar ta Saudiya jamian Amurka sunce mayakan islama suna shiga Iraqi daga kasashen Qatar da Yemen ta cikin kasa abokiyar gabar Amurkan wato Syria.

Su dai jamian na Amurka biyu Gates da Rice zasu tattauna yadda kasashe makwabta zasu taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Iraqi.

A wani yunkuri kuma na lafarda damuwa da yan sunni masu goyon bayan Amurka suke nunawa game da kasar Iran,gwamnatin Amurka zata tattauna batutuwan taimako da sayarda makamai ga wadannan kasashe.

A cewar jamian gwamnatin Amurka yarjejeniyar sayarda makaman za’a kulla ta ne da nufin kara karfafawa kawayen Amurka a yankin gabas ta tsakiya wajen fuskantar kasar Iran.

Sai dai kuma wani babban jamii na maiakatar tsaron Amurkan yace kawayen Amurka a yankin basu yarda da Amurka ba saboda haka zai yi wuya su bada hadin kansu gaba daya game da shirin da Amurka take da shi game da yankin.

Gwamnatin Amurkan tana shirin sanarda jerin yarjeniyoyinta na sayarda makamai da kudinsu ya kai dala biliyan 20 tsakaninta da kasashen Saudiya da wasu kasashe 5 na yankin gulf.

Sai dai kuma kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty tayi suka ga wannan yunkuri,Mathias John wakili ne na kungiyar anan Jamus.

„muna ganin wannan ba alama ce mai kyau ba a wannan lokaci ayi batun sayarda makamai ga wasu kasashen yankin,musamman kasashe da aka sani suna keta hakkin bil adama,muna ganin bai kamata a basu makaman ba domin zasu iya nafani da su wajen ci gaba da keta hakkin bil adama“

A nashi bangare wakilin ofishin jakadancin Israila a birnin Berlin Ilan Mor ko ma dai dame halinda ake ciki a yankin gabas ta tsakiya batu ne halin tsaka mai wuya kot a wace hanya aka bi.

„ tambayata anan iatce wane abu ne mafi muni,batun makamai ne na alada ko kuma na nukiliya,abinda muke so nan shine a kawarda koda wane irin makamai ne,ainihin halinda ake ciki a yankin gabas ta tsakiya shine a kullum muna cikin halin tsaka mai wuya,zabi ne kamar tsakanin cutar kwalara da annoba“

Rice da Gates dai ana sa ran zasu gana da ministocin Saudiya da Qatar da Kuwait da Bahrain da kuma Oman da ita kanta kasar Masar a gurin shakatawa na Sharm el sheikh.

Daga bisani Rice zata wuce zuwa birin Jerusalem da Ramalla inda zata gana da jamian Israila da na Palasdinu.