1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Rice a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus wato Angela Merkel da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice , sun ci alwashin yin aiki kafada da kafada don warware takaddamar data taso game da hukumar CIA.

Cimma wannan yarjejeniya tazo ne a yayin da gwamnatin ta Jamus ke bukatar cikakkikyar amsa daga mahukuntan na Amurka game da zargin da ake cewa hukumar leken asiri ta CIA na mallakar wasu gidajen azabtar da fursunoni a wasu kasashe a nahiyar ta turai.

Ba a dayan haka akwai kuma zargin da akeyiwa hukumar ta CIA cewa tana amfani da wasu filayen jiragen sama na Jamus wajen yin jigilar fursunonin izuwa asirtattun gidajen azabtarwar dake wasu kasashe a gabashin Turai.

Kafin dai gudanar da taron manema labaran sai da shugabannin biyu suka yi wata ganawar keke da keke a safiyar yau talatar.

A waje daya kuma Kafin tashin ta izuwa wannan ziyara, CR ta karyata zargin da akewa Amurka cewa tana take hakkin fursunon